Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙungiyar Manoma ta Nijeriya (AFAN), Dakta Farouk Rabiu Mudi, ya sake jaddada cikakken goyon bayan ƙungiyar ga Ajandar Sabonta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na sauya fasalin harkar noma da tabbatar da wadatar abinci a ƙasar.
Mudi ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai, inda ya ce AFAN, a matsayinta na babbar ƙungiyar da ke haɗa manoma, ƙungiyoyin kayan amfanin gona, ƙungiyoyin haɗin gwiwar manoma da sauran hukumomi masu alaƙa da noma, ta ƙuduri aniyar yin aiki tare da gwamnatin yanzu domin magance matsalar ƙarancin abinci tare da buɗe babbar damar da Nijeriya ke da ita a fannin noma.
Ya ce Nijeriya na da fiye da hekta miliyan 70 na filayen noma, sai dai wasu wuraren da a baya ake noma sun kasance cikin barazana sakamakon mamayar miyagun mutane.
A cewarsa, ko da yake gwamnatin da ta gabata ta yi ƙoƙari sosai wajen dawo da waɗannan yankuna ƙarƙashin ikon jama’a, ƙudirin gwamnatin yanzu na tabbatar da tsaron gonaki ya kawo sauƙi ga manoma da dama, musamman ta hanyar haɗa kai tsakanin hukumomin tsaro ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu.
Mudi ya ce, haɗin gwiwar Ma’aikatar Tsaro ta Tarayya da AFAN shi ma ya zama wani muhimmin sauyi ga manoma, domin hakan ya fara bai wa manoma damar komawa gonakinsu bayan tsawon lokaci.
Ya ƙara da cewa ana samun sauye-sauye a sansanonin ’yan gudun hijira na cikin gida (IDP), yayin da aka mayar da yawancin mutanen da rikici ya raba da muhallansu zuwa gidajensu.
Ya bayyana wannan mataki a matsayin abin yabawa, yana mai cewa: “A matsayinmu na nuna godiya, kwanan nan an ba Janar Christopher Gwaban Musa sarautar Mai Kula da AFAN (Patron), abin da ya samu gagarumar karɓuwa a Abuja.”
Shugaban AFAN ya bayyana cewa hacin gwiwar ƙungiyar da Ma’aikatar Tsaro ta Tarayya ya kuma ba da damar kai wasu daga cikin shugabannin ƙungiyar rangadin nazarin harkar noma zuwa Brazil, inda suka halarci bikin baje kolin kasuwanci na shekara-shekara na ƙasar, Cotrijal.
Ya ce manufar wannan rangaɗi ita ce nazarin sabbin dabaru da fasahohin da za su taimaka wa manoman Nijeriya su koma gonakinsu, tare da samar da hanyoyin ƙirƙire-ƙirƙire na tallafa wa mutanen da har yanzu suke rayuwa a sansanonin ’yan gudun hijira.
Mudi ya kuma sanar da cewa AFAN, ƙarƙashin jagorancinsa, za ta shirya Baje Kolin Noma na ƙasa da ƙasa tsakanin Nijeriya da Brazil a watan Nuwamba na wannan shekara, tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Kano da ƙungiyar ’Yan Kasuwa, Masana’antu, Ma’adinai da Noma ta Jihar Kano (KACCIMA).
Ya ce Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya, Ma’aikatar Raya Kiwo, Ma’aikatar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, da kuma Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya duk suna haɗin gwiwa wajen ganin an cimma wannan buri.
A cewarsa, shirin na da nufin sauya harkar noma da kiwo daga noma na dogaro da kai zuwa noma mai amfani da injuna, wanda zai iya mayar da Nijeriya babbar cibiyar noma a yankin Yammacin Afirka.
Mudi ya ce ƙulla alaƙa da manoman Brazil, tare da shirin AFAN da Gwamnatin Tarayya na ƙara zuba jari a shirye-shiryen Out-grower da tsarin samar da kuɗin noma ta haɗin gwiwar hanyoyin kuɗi, zai taimaka wajen farfaɗo da sassan noma da kiwo.
Ya yi nuni da cewa ƙasashen da suka rungumi irin waɗannan tsare-tsare sun samu ci gaba tare da ƙara yawan Jimillar Abin da ƙasa ke Samarwa (GDP) a duk shekara.
Shugaban AFAN ya ce haɗin gwiwar da ƙungiyar ke yi da hukumomin Gwamnatin Tarayya, kamfanoni masu zaman kansu da abokan hulɗar ci gaba zai taimaka wajen hanzarta mayar da Nijeriya ɗaya daga cikin wuraren da suka fi jan hankalin masu zuba jari a harkar noma.
Ya ce Nijeriya na da isassun filayen noma da kuma ɗimbin mutanen da suke da sha’awar yin noma a matakin kasuwanci, musamman domin samar da amfanin gona mai yawa da za a iya fitarwa zuwa ƙasashen waje.
Mudi ya ce AFAN a shirye take ta karɓi duk wata sabuwar dabara ko ƙirƙire-ƙirƙire da za ta taimaka wa ƙananan manoma.
Ya ƙara da cewa, ta hanyar ƙoƙarin gwamnatocin jihohi wajen samar da ayyukan ƙara wa manoma ilimi da dabarun noma (agricultural eɗtension services), AFAN za ta tabbatar da cewa manufar gwamnatin Tinubu ta magance matsalar ƙarancin abinci ta tabbata.
Ya yaba wa Shugaba Tinubu kan kafa Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya, Ma’aikatar Raya Kiwo da Ma’aikatar Tattalin Arzikin Teku (Blue Economy), tare da tallafa wa Shirin NAGS-AP, Asusun Raya Noma na Nijeriya da Bankin Noma.
A cewarsa, idan aka tafiyar da waɗannan shirye-shirye yadda ya kamata, za su iya kawo gagarumin sauyi a harkar noma ta Nijeriya.
A ƙarshe, Mudi ya yi kira ga dukkan mambobin AFAN da su rungumi manufofin ƙungiyar da na Gwamnatin Tarayya, su yi amfani da sabbin dabarun da gwamnati ta ɓullo da su, tare da neman shawarwari da tallafi daga hukumomin da abin ya shafa.
Ya ce, “A wannan lokaci, ina kira ga dukkan mambobinmu a faɗin ƙasar nan da su goyi bayan sauyin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke ƙoƙarin kawo wa harkar noma, domin mu buɗe kyawawan damar da Allah Ya hore mana.”
Ya kuma gode wa manema labarai bisa sauraron saƙon ƙungiyar, kafin ya kammala da taken da AFAN ke amfani da shi wajen ƙarfafa manoma, wato “Babu manomi, babu ƙasa.”
