Yadda hukumar bogi ta gina tsarin gudanarwa a jihohi 20 da ofisoshi a Amurka da Chana

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‘National Brands Development and Made in Special Project Offic’, wadda aka zarga da “hukumar bogi”, ta kasance ta faɗaɗa tsarin gudanarwarta a jihohin Nijeriya 20 da wasu manyan ƙasashe guda biyu gami da samar da kodineta ja ƙasa, daraktocin shiyyoyi, kodentocin jihohi da wakilai a Amurka da Chana, kamar yadda binciken jaridar NewsPointNigeria ya nuna.

A wani bincike da aka gudanar a shafinta na intanet a ranar Asabar, 22 ga Agusta, 2026, an gano cewa Hon. Nwabueze George shi ne shugabanta kuma kodineta na ƙasa tare da daraktan gudanarwa na ƙasa, daraktocin shiyyoyi uku, kodentocin jihohi 20 da wakilai da aka tura Amurka da Chana.

Hakan na zuwa ne bayan da a ranar Juma’a, Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa, Musa Aliyu ya ce Shugaba Bola Tinubu ya umarci da a gaggauta kamo George Nwabueze da hukumar ta bayyana a matsayin “jagora” na ofishin.

Haka kuma, Tinubu ya bayar da umarnin dakatar da manyan sakatarori M.S. Danjuma, Nadungu Gagare da Richard P. Pheelangwah bayan gano ƙagaggiyar hukumar, wadda ICPC ta ce an ba ta guri a farfajiyar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) ba tare da sahalewar Fadar Shugaban Ƙasa ba.

Hukumar ICPC ta kuma ce an gano cewa jagoran yana amfani da sunaye kamar haka: George Nathan Nwabueze, George Nwabueze, George Buchi Nwabueze, Prince George Buchi Nwabueze da kuma George Nwabueze.

Sannan, a shafin an zayyano Dakta Bassey B. Unaowo wanda shi ne mai taimaka wa babban sakatare na musamman kan lamuran siyasa da tattali na OSGF; Dakta Hajara Njidda Amoni a matsayin daraktar gudanarwa ta ƙasa; Mista Oladunjoye Musiliua a matsayin daraktan shiyya na Kudu maso Kudu; Hafsat Sahabi Dange a matsayin daraktar shiyyar Arewa; da kuma Misis Ugochi Akudo Nwosu da na Kudu maso Gabas.

Bincike a shafin ya kuma cewa waɗannan mutane a matsayin kodinetocin jihohi:
“Katsina: Dr Babangida Kabir Ruma
Kaduna: Hon. Abdulhaleem Ishaq Ringim
Delta: Hon. Dr Godwin Adolor
Kebbi: Hussaini Abdullahi, Esq., FSI
Osun: Hon. Olugbemi Adetola Adelowokan
Anambra: Hon. Chiamaka Nnake
Nasarawa: Hon. Osolafia Muhammed, PhD
Plateau: Mrs Salome Audu Bidda
Benue: Hon. Orduen Andrew Ikon
Ondo: Amb. Orioye G. Benedict
Ogun: Hon. Engr. Kehinde Akintonide, FNSE
Sokoto: Hon. Ibrahim Umar Aliyu
Abia: Hon. Mrs Nwosu Chinyere R.
Zamfara: Hon. Ibrahim Bello Marafa
Niger: Haj. Zainab Mohammed
Kano: Hon. Abubakar Ahmad Bichi (Khalifa)
Taraba: Hon. Justin Aondoaseer Tyopuusu
Oyo: Alhaji Bello Kolawole Ghaffar, FCA
Bauchi: Hon. Farouq Siyi
Kogi: Hon. Olorukooba Bidemi”

Wannan ci-gaba na zuwa ne yayin da ake tsaka da bincike kan ƙagaggun hukumomin bogi. Da fari dai ICPC ta gano Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) da wasu biyu a matsayin na bogi – the FCT Investment Promotion Agency and the Foreign Investment Promotion Agency, yanzu kuma wannan.

By Babaji

Leave a Reply