Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta nemi goyon bayan al’umma domin sake komawa wa’adi na biyu ne bisa ayyukan da ta gudanar da nasarorin da ta samu, ba wai ta hanyar yin sabbin alƙawurra ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bikin ƙaddamar da masu gudanar da ayyukan APC Zalla Movement a ƙananan hukumomi 34 da mazaɓu 361 na jihar Katsina, wanda aka gudanar a People’s Square, Katsina, domin ƙara ƙarfafa tsarin jam’iyyar APC tun daga matakin ƙasa.
Gwamna Raɗɗa ya ce nasarorin da gwamnatinsa ta samu a sassa daban-daban na jihar sun ba ta damar komawa wajen al’umma da tarin ayyukan da ta gudanar.
Ya ce: “A yau, al’umma ba sa kallon alƙawurra kawai a zaɓe mai zuwa, za mu nuna wa jama’a abin da muka aikata, ba wai mu yi masu sabbin alƙawurra ba.”
Gwamnan ya ƙara da cewa ayyukan raya ƙasa sun isa al’ummomi a faɗin jihar, yana mai cewa kusan kowace mazaɓa ta samu wani nau’i na tallafi ko aikin ci gaba daga gwamnatinsa.
Ya ce: “A cikin mazaɓu 361 na Jihar Katsina, babu wata mazaba da ba ta da aikin da wannan gwamnati ta aiwatar.”
Gwamna Radda ya bayyana ƙaddamar da ƙungiyar a matsayin wani muhimmin mataki na ƙara haɗin gwiwa tsakanin APC Zalla Movement da sauran tsarin jam’iyyar APC.
Ya buƙaci sabbin shugabannin da aka ƙaddamar da su kasance masu jajircewa, dogaro da kai da kuma mayar da hankali wajen ƙarfafa jam’iyyar a matakin ƙasa.
Haka kuma, ya buƙaci ƙungiyar ta ci gaba da wayar da kan jama’a, musamman wajen kai bayanai game da shirye-shiryen gwamnati da ayyukan ci gaba kai tsaye zuwa ga al’ummomi.
Gwamnan ya tabbatar da goyon bayan gwamnatinsa ga ƙungiyar, tare da sanar da cewa za a samar mata da motoci ga shiyyoyin ƙungiyar guda uku, domin sauƙaƙa ayyukanta da gudanar da gangamin wayar da kan jama’a.
Ya kuma yi kira ga shugabannin jam’iyya da magoya bayanta da su haɗa kai wajen kare tare da ƙarfafa amanar da al’umma ta ba gwamnati.
A nasa ɓangaren, tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Architect Ahmed Musa Dangiwa, ya buƙaci sabbin shugabannin ƙungiyar da su kasance masu jajircewa wajen tabbatar da nasarar APC a kowane mataki.
Shugaban APC na Jihar Katsina, Hon. Bishir Gambo Saulawa, ya yabawa marigayi Dr. Bala Nuhu Kankia bisa kafa ƙungiyar, yana mai cewa ta kasance wata hanya ta ƙarfafa jam’iyyar da kuma wayar da kan jama’a game da nasarorin Gwamna Raɗɗa da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Shi ma Darakta-Janar na APC Zalla Movement, Dr. Bala Nuhu Kankia, Sadaukin Kankia, ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa ƙaddamar da shugabannin ƙungiyar a ƙananan hukumomi 34 da mazaɓu 361.
Ya ce ƙungiyar za ta mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a game da manufofi da shirye-shiryen APC, tare da isar da bayanai kan ayyukan gwamnati, ciki har da Community Development Programme (CDP), KASEDA, da shirye-shiryen kiwon lafiya, ilimi, noma da tsaro zuwa matakin ƙasa.
An gudanar da taron ne tare da halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin APC, ‘yan siyasa, masu ba gwamnati shawara, shugabannin matasa da mata, magoya bayan jam’iyya da sauran al’umma.
