Gimbiya Elayo ta kira al’umma su kare aikin ACReSAL a Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Gimbiya Margaret Elayo kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa kuma shugabar kwamitin gudanarwa na aikin ACReSAL a jihar Nasarawa ta yi kira na musamman ga al’ummomin da suka amfana a faɗin jihar da su ɗauki nauyin kiyayewa da kula da kuma kare dukkan ayyukan da aka yi musu ta hanyar ayyukan “Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes” (ACReSAL) a turance wato wani shiri na musamman dake kare muhalli da kuma rayukan al”umma musamman a yankunan karkara domin cigaba mai ɗorewa.

Dr. Elayo ta yi wannan kiran ne a ranar ƙarshe na yawon duba ayyukan ACReSAL a faɗin jihar inda ta kai ziyara gonar Maisauri da ke ƙaramar hukumar Kokona da kuma al’ummar Kougbarou da ke ƙaramar hukumar Karu. Ta jagoranci mambobin kwamitin gudanarwa da na fasaha na jihar tare da tawagar aikin ACReSAL domin tantance yadda ayyukan ke gudana da kuma tasirin su.

A lokacin duba ayyukan dasa bishiyoyi da sauran ayyukan muhalli a cikin waɗannan al’umma biyu kwamishiniyar ta yi magana da wakilain al’umma da mata da kuma masu amfana dake da alhakin kulawa da ɗorewar waɗannan zuba jari.

Wakilain al’ummomin sun nuna godiya ga gwamnatin Injiniya Abdullahi A. Sule bisa ayyukan cigaba da aka kawowa ta hanyar ACReSAL din. Sun ce ayyukan sun yi tasiri mai kyau wajen inganta rayuwa da ɗorewar muhalli da bunƙasa al’umma inda duka kuma roƙi a ƙara ba su dama da cigaba da ayyukan tare da yin alƙawarin cigaba da karewa da kula da kayan aiki da zuba jarin da aka ba su.

Da take mayar da martani Dr. Elayo ta yaba wa al’ummomin bisa jajircewarsu da halartarsu. Ta tabbatar musu cewa gwamnati za ta cigaba da kasancewa tare da su da ba su goyon baya da yanayi zaman lafiya da faffaɗan ƙasa da kuma albarkatun da al’ummomin ke da su na ba da babbar dama ga ƙara bunƙasa da zuba jari.

Kwamishiniyar ta ƙara jaddada wa masu amfana da cewa su ɗauki ayyukan ACReSAL ba kawai a matsayin ayyukan gwamnati ba sai dai a matsayin dukiyar al’umma da ke buƙatar haɗin kai da kariya da kulawa ta dindindin.

A nasa ɓangaren mai ɗaukar nauyin aikin ACReSAL na jihar Nasarawa Dr. Elias Gyobe Napoleon ya buƙaci al’ummomin da su cigaba da jajircewa wajen tabbatar da ɗorewar ayyukan, su kuma ɗauki cikakken nauyin zuba jari.
Yace al’ummomin su ne masu amfana na farko da na kusa don haka dole ne su taka rawa wajen karewa da kula da su.

Ya jaddada cewa idan al’umma sun ɗauki nauyin aikin da kansu ba wai za su kiyaye abin da ke hannunsu ba ne kawai har ma za su buɗe ƙofa ga samun ƙarin ayyukan cigaba nan gaba.

Ziyarar ta ƙarƙare ne da nuna yadda ake inganta girman shuka da kiyaye danshi wanda kwamishiniyar da mai ɗaukar nauyin aikin suka yi tare. Wannan nunawa ta ƙara ƙarfafa muhimmancin amfani da hanyoyin da suka dace na muhalli domin tabbatar da girma mai kyau da ɗorewar ayyukan dasa bishiyoyi kamar yadda Dr. Gyobe ya bayyana.

By ukarofi

Leave a Reply