NSCDC da ma’aikatar muhalli ta Nasarawa sun haɗa kai don yaƙi da shigar yara haƙar ma’adanai

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa ta jihar Nasarawa ta haɗa kai da hukumar tsaro ta NSCDC domin magance matsalar shigar ƙananan yara cikin harkar haƙar ma’adanai tare da kai farmaki kan masu haƙar ma’adanan ba bisa doka ba.

An ƙulla wannan yarjejeniyar ne a ranar juma’a yayin wani ziyara na musamman da kwamandan NSCDC na jihar Nasarawa Brah Samson Umorou ya kai wa ofishin kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa Gimbiya Dr. Margaret Elayo.

A lokacin zaman Dr. Elayo ta bayyana abubuwan da ta gani da ido a yayin ziyarar tantance illolin muhalli da ta kai wuraren haƙar ma’adanai.
Ta bayyana alhini bisa ganin ƙananan yara da ya kamata su kasance a makaranta suna aiki a cikin ramin haƙar ma’adanai masu haɗari da firgita.

Kwamishiniyar ta bayyana halin a matsayin “mummunar lamari” da zai iya haifar da mummunar illa idan aka bari haka. Don haka ta roƙi kwamandan Umorou da ya taimaka mata wajen ceto waɗannan yara da hana su shiga harkar haƙar ma’adanai.

Baya ga haka Dr. Margaret Elayo ta kuma bayyana damuwarta kan yawaitar sansanonin haƙar ma’adanai da ake cigaba da kafawa a jihar ba doka, inda ta gargaɗi cewa suna haifar da barazanar tsaro mai girma.
Ta jaddada buƙatar NSCDC ta taimaka cikin gaggawa wajen rushe wadannan sansanoni domin kare al’umma.

A nasa ɓangaren kwamandan rundunar NSCDC a jihar ta Nasarawa Brah Samson Umorou ya tabbatar wa kwamishina Dr. Elayo da shirye-shiryen jami’an sa na magance wannan matsala mai matuƙar gaggawa. Yace za su ɗauki mataki mai ƙarfi kan duk wani aiki dake kawo barazana ga zaman lafiya da tsari a jihar.

By ukarofi

Leave a Reply