Kwastom ta miƙa bindiga 399 da aka ƙwace ga ofishin Ribadu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kwastom ta Nijeriya ta miƙa bindiga guda 399 da aka ƙwace tare da tarin wasu muhimman kayayyakin bindigogi, ga Ofishin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, bayan kammala bincike kan wani katafaren makaman da aka tare a tashar jiragen ruwa ta Tsibirin Tincan da ke Legas.

Shugaban Hukumar Kwastom ta Nijeriya, Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya ce an kammala haɗa bindigogin da aka tarwatsa tare da gudanar da cikakken bincike kan kayayyakin da aka kama.

A cewarsa, binciken ya tabbatar da cewa kayan sun ƙunshi bindigogi ƙirar Jojef guda 399 da aka riga aka haɗa, baya ga wasu muhimman sassan bindigogi. Adeniyi ya ce, cikakken lissafin kayayyakin da aka ƙwace ya kuma gano frames 89, heat shields 16, trigger pins 10, pistons uku, locking lugs 25, charging handles 80, pistol-grip screws 39, springs 34, trigger groups 57, foregrip latches 66, foregrips ko handguards 45, pistol grips huɗu da barrels biyar.

Shugaban Kwastom ya bayyana cafke makaman a matsayin babban cikas ga harkar safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, yana mai gargadin cewa ƙungiyoyin masu aikata laifuka na iya ƙoƙarin amfani da iyakokin ƙasa, tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama wajen shigo da haramtattun kayayyaki yayin da Nijeriya ke gab da shiga wani sabon zagayen babban zaɓe. Ya ce, hukumar za ta ƙara tsaurara sa ido da ayyukan tabbatar da doka domin daƙile irin waɗannan yunƙure.

“Muna daf da shiga wani muhimmin zagayen zaɓe, kuma mun san cewa a irin wannan lokaci masu aikata laifuka za su so amfani da iyakokinmu, tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama wajen shigo da kayayyaki irin waɗannan. Za mu ƙara kaimi wajen tabbatar da cewa ba mu bari hakan ta faru ba,” inji Adeniyi.

Ya kuma jaddada cewa Hukumar Kwastom ta Nijeriya za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri wajen gudanar da ayyukanta, tare da ƙarfafa sa ido a kan iyakoki da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin gano tare da tarwatsa hanyoyin safarar makamai.

A cewarsa, wannan haɗin gwiwa zai haɗa da ci gaba da aiki tare da Cibiyar ƙasa ta Kula da ƙananan Makamai da Makamai Masu Sauƙin ɗauka (NCCSALW), wadda ke ƙarƙashin Ofishin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro.

Bayan kammala tantancewa da ƙididdigar makaman, Adeniyi ya miƙa su a hukumance ga Darakta-Janar na Cibiyar Kula da ƙananan Makamai da Makamai Masu Sauƙin ɗauka, ƙarƙashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.

Ya ce wannan miƙa makaman na nuna haɗin kan hukumomin tsaro wajen tabbatar da cewa irin waɗannan muggan makamai ba su samu hanyar shiga hannun jama’a ba, tare da gano, bin diddigin da gurfanar da waɗanda ke da hannu a safarar su. Adeniyi ya kuma bayyana cewa mutane biyu da aka kama a matakin farko na binciken makaman, an miƙa su ga Ofishin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.

Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan yiwuwar yawaitar safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba gabanin zaɓen shekarar 2027. Hukumar Kwastom ta ce za ta ƙara tsaurara matakan tsaro a iyakoki, tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama domin hana masu aikata laifuka amfani da lokacin zaɓe wajen shigo da haramtattun makamai.

By ukarofi

Leave a Reply