Majalisar NSDC ta jawo jarin Dala biliyan ɗaya don Nijeriya ta daina dogaro da sukarin waje

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar Bunƙasa Masana’antar Sukari ta ƙasa (NSDC) ta ƙara ƙaimi wajen jawo jarin masana’antar sukari, inda ta ƙulla haɗin gwiwar zuba jari na Dala biliyan 1 da kamfanin SINOMACH na ƙasar Chana, domin hanzarta samar da sukari a cikin gida da rage dogaro da shigo da shi daga ƙasashen waje.

Haɗin gwiwar na daga cikin shirin Asusun Hanzarta Ayyukan Sukari na Naira biliyan 10, wanda NSDC ta kafa tare da Bankin Masana’antu a ƙarƙashin Shirin Haɗa Samar da Kayayyaki a Cikin Gida (BIP).

Babban Sakatare kuma Babban Daraktan NSDC, Kamar Bakrin, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, bayan wata ziyarar girmamawa da tawagar reshen Abuja na Cibiyar Daraktocin Kamfanoni ta Chartered (CIoD) ta kai wa majalisar.

Bakrin ya ce, Nijeriya na amfani da kusan tan miliyan 1.8 na sukari a duk shekara, yayin da ake kiyasta cewa kusan dala biliyan 1 na fita daga ƙasar a kowace shekara wajen biyan kuɗin sukari da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje.

Sai dai ya ce, NSDC ba ta kallon wannan giɓin a matsayin matsalar da za a yi ta ƙorafi a kai, illa wata babbar kasuwa ce da tuni take nan a cikin gida, wadda ya kamata masu samar da sukari na Nijeriya su dawo su mallake ta.

Bakrin ya ce, manufar Tsarin Jagororin Masana’antar Sukari ta Nijeriya na NSMP 2.0 ita ce a riƙe darajar kuɗin da ake samu daga masana’antar a cikin tattalin arzikin ƙasa, ta hanyar samar da ayyukan yi, ƙara kuɗin shiga ga al’ummomin karkara, rage fitar da kuɗin waje da kuma gina ƙarfin masana’antu.

Ya ce, babbar matsalar masana’antar sukari a tarihi ba rashin manufofi ba ce, sai dai gazawar aiwatar da manufofin yadda ya kamata.

“Ba mu rasa manufofi ba. Abin da muka sha fama da shi shi ne aiwatarwa bisa aa’idojin duniya. Matsalar ba ta shafi noma kawai ba ce; matsalar shugabanci da gudanarwa ce, kuma cibiyoyi masu nagarta da tsari za su iya magance ta.”

Ya bayyana NSMP 2.0 a matsayin “shirin hanzartawa”, wanda ke da burin gajarta lokacin da Nijeriya za ta ɗauka kafin ta samu wadatar sukari daga abin da ake samarwa a cikin gida.

A cewarsa, shirin na da burin samar da kusan tan miliyan biyu na sukari a cikin gida. Bakrin ya ce burin majalisar ya wuce maye gurbin sukari da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje. Ya bayyana noman rake a matsayin ɗaya daga cikin amfanin gonar da ke da fa’idoji masu yawa, domin baya samar da sukari kaɗai; ana iya samun ethanol, abincin dabbobi da wutar lantarki daga cikinsa.

Saboda haka, ya ce NSMP 2.0 an tsara shi ne domin Nijeriya ta amfana da dukkanin sassan wannan tsarin samar da kaya, daga noman rake har zuwa sarrafa shi da samar da kayayyaki daban-daban.

Dangane da matakan tabbatar da bin ƙa’ida, Bakrin ya ce an sake fasalta Shirin Haɗa Samar da Kayayyaki a Cikin Gida (BIP) bisa wasu muhimman ƙa’idoji guda huɗu: cancanta, lada, tabbatarwa da sa ido. Ya ce manufar tsarin ita ce tabbatar da cewa duk wani gata da gwamnati ta bai wa masu zuba jari, musamman damar samun kaso daga kasuwar sukari, yana tafiya ne tare da ainihin samar da sukari a ƙasa.

Wannan na nufin ba za a bai wa kamfani gata ko kaso bisa takarda kawai ba tare da an tabbatar da cewa yana gudanar da ainihin ayyukan samar da sukari ba.

Babban Daraktan ya ƙara da cewa Asusun Hanzarta Ayyukan Sukari na Naira biliyan 10, wanda aka kafa tare da Bankin Masana’antu, zai taimaka wajen ɗaukar nauyin binciken yiwuwar aiwatar da ayyukan da kuma shirye-shiryen fara manyan ayyukan masana’antar. A cewarsa, hakan zai sauya wuraren da ba a fara aikin masana’antu a kansu ba zuwa cikakkun ayyukan da za su kasance a shirye domin masu zuba jari.

Daga nan ne za a haɗa irin waɗannan ayyuka da yarjejeniyar dala biliyan 1 ta EPC da tallafin kuɗi da aka ƙulla da SINOMACH na China, wadda za ta samar da hanyar gina ayyukan tare da samun kuɗin gudanar da su bayan an kammala shirye-shiryen.

Shugabar tawagar Cibiyar Daraktocin Kamfanoni ta Chartered, Fatima Mede, ta yaba da jagorancin NSDC da kuma sauye-sauyen da take jagoranta a masana’antar sukari. Ta ce, ci gaban da ake samu wajen kai Nijeriya ga wadatar da kanta da sukari abin a yaba ne, tare da tabbatar da cewa cibiyar a shirye take ta yi aiki tare da NSDC a dukkan fannonin da suka shafi muradunsu na bai ɗaya. Ta ce hakan wani ɓangare ne na gudunmawar CIoD wajen taimaka wa ci gaban masana’antar sukari da bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.

By ukarofi

Leave a Reply