Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dokokin Tarayyar Nijeriya na da ma’aikata sama da 14,000, ban da ’yan majalisar tarayya 469 da kuma ɗimbin baƙi da ke ziyartar majalisar, lamarin da ya sanya ta zama ɗaya daga cikin majalisun da suka fi yawan ayyuka a duniya.
Magatakardar Majalisar Dokokin Nijeriya (CNA), Kamoru Ogunlana, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin taron ƙarshe na shirin ƙara wa mataimakan ’yan majalisa ƙwarewa a Majalisa ta 10.
Ogunlana ya ce, yawan ma’aikatan majalisar, ’yan majalisa da kuma baain da ke ziyartar majalisar a kullum ya sa gudanar da ayyukan majalisar tarayya ya kasance babban aiki mai matuaar buƙatar ingantaccen tsari. Ya ce: “Babu wata majalisa a duniya da ke da yawan aiki kamar Majalisar Dokokin Nijeriya, wadda ke da ma’aikata sama da 14,000, ban da ’yan majalisar tarayya da baƙinsu.”
Magatakardan ya kuma bayyana cewa Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai sun zartar da jimillar ƙudirin dokoki 3,500 cikin shekaru uku da suka gabata. A cewarsa, Majalisar Dattawa ta zartar da ƙudirin dokoki 1,500, yayin da Majalisar Wakilai ta zartar da 2,000. Ya ce yawan ayyukan dokoki da majalisar ke gudanarwa na ƙara nuna muhimmancin samar da ingantaccen tsarin tallafi da zai bai wa ’yan majalisa damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ogunlana ya sake yin kira da a samar da tsarin albashi na musamman ga mataimakan ’yan majalisa, yana mai bayyana su a matsayin muhimman ginshiƙai wajen gudanar da ayyukan majalisa. Ya buƙaci Hukumar Kula da Ayyukan Majalisar ƙasa (NASC) da Hukumar Tattara Kuɗaɗen ƙasa da Rarraba Su (RMAFC) da su warware matsalolin da suka shafi albashi da kuma yanayin aikin mataimakan ’yan majalisar.
Ya ce: “Akwai buƙatar fayyace tare da daidaita nauyin da NASC da RMAFC ke da shi wajen tsara albashi da yanayin aikin mataimakan ’yan majalisa.”
Ogunlana ya bayyana cewa yayin da NASC ke da alhakin naɗa mataimakan ’yan majalisa da kula da harkokinsu na gudanarwa, batun albashinsu yana tafiya ne bisa tsarin da RMAFC ta tsara ko ta amince da shi, sannan Majalisar Dokokin ƙasa ta amince da shi. Ya kuma ce naɗin mataimakan ’yan majalisa na ɗan lokaci ne kuma ba ya ba su damar samun fansho bayan ritaya, inda ya yi kira da a sake duba tsarin domin inganta jin daɗinsu da kuma ƙara musu ƙwarewar da za ta taimaka wajen tallafa wa ’yan majalisa wajen gudanar da ayyukansu.
