Yadda na ceci Obasanjo daga allura mai kisa a kurkuku – Atiku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan takarar jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya yi iƙirarin cewa ya ceci tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo daga wani yunƙuri na halaka shi da wata allura mai kisa a lokacin da su biyun suke kurkuku a zamanin mulkin soji.

Atiku ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai a ranar Alhamis, 20 ga Agusta, 2026, inda ya ce shi ya fitar da labarin shirin halaka Obasanjo kuma ya gargaɗe shi da cewa kada ya bari a masa kowacce kalar allura.

A cewar Atiku, an taɓa kitsa irin makircin akan marigayi Janar Shehu Musa Yar’Adua. Ya ce, lokacin da ya gano cewa ana neman rayuwar Obasanjo ta irin salon, sai ya ankarar da shi. “Na ceci rayuwar Obasanjo a kurkuku ta hanyar fitar da labarin wata allura da da ta halaka shi. Sun yi irin haka ga Yar’Adua, kuma a lokacin da na gano suna shirin yi masa, na gargaɗe shi da cewa kada ya bari a masa allurar,” inji Atiku.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya fitar da batun ne kan rikicinsa na kwanan nan da Obasanjo, inda ya ce tsohon shugaban ƙasar yana so duniya ta tsane shi ne saboda ya ƙi goyon bayan shirin wa’adi na uku a kujerar shugaban ƙasa na Obasanjo.

Atiku da Obasanjo sun jagoranci Nijeriya daga 1999 zuwa 2007, saidai daga bisani alaƙarsu ta yi tsami bisa rashin nasarar shirin yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima ta yadda zai bayar da damar wa’adi na uku ga shugaban ƙasar.

Wannan iƙirari na zuwa ne gabanin zaɓen 2027 yayin da ake cigaba da tayar da tsofaffin tsama a tsakanin manyan ‘yan siyasa, lamarin da ke bai wa al’umma damar tafka muhawara akansu.

By Babaji

Leave a Reply