Gwamnatin Tarayya ta bada hutun Mauldin 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata, 25 ga Agusta, 2026 a matsayin ranar hutun Mauldin 2026 domin karrama lokacin zagayowar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana haka a yau Jumma’a a wata sanarwa da ya fitar da hannun Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani.

Ministan ya taya al’ummar Musulmin Nijeriya da wasu sassan duniya murnar zagayowar lokacin, yana mai kira a gare su da su yi amfani da damar hakan wajen nuna tasirin karantarwar Annabi Muhammad a harkokin rayuwarsu na yau da kullum.

Ya ce, kowane bikin Mauldi na ba wa ‘yan Nijeriya damar ɗaukar muhimman darussa daga rayuwar Annabin tsira, musamman wajen sadaukarwa da nuna tausayi acikin al’umma.

Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi amfani da lokacin wajen yi wa ƙasa addu’o’in samun zaman lafiya, haɗin kai da dunƙulewa waje guda domin samun ci-gaba mai ɗorewa.

Kazalika, ya jaddada ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na bai wa rayuka da dukiyoyin al’umma kariya da kuma bunƙasa zaman lafiya da ɗorewa a sassan ƙasar.

By Babaji

Leave a Reply