An buƙaci Akanta Janar ya binciki EFCC bisa tsare ɗalibar ajin ƙarshe a BUK, Maryam Shehu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Lauyan kare ‘yancin ɗan-adam, Abba Hikima, ya kirayi Antoni Janar na Ƙasa (AGF), da ya gaggauta shiga tsakani cikin lamarin Maryam Isah Shehu, wadda ɗalibar ajin ƙarshe ce ta Jami’ar Bayero da ke Kano, yana mai bayyana tsawaita cigaba da tsare ta da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ke yi a matsayin saɓa wa doka da hukunce-hukuncen dokokin ‘yancin ɗan-adam na Nijeriya.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Soshiyal Mediya a ranar Alhamis, Abba Hikima ya caccaki salon yadda EFCC take gudanar da al’amarin ɗalibar, inda ya zarge ta da tsare ɗalibar har na tsawon kwanaki 35 kafin shigar da tuhuma guda akanta.

A cewarsa, an shigar da ƙorafin ne bayan ƙasa da kwana ɗaya da aka riƙa yaɗa damuwa a fili kan cigaba da tsare ta ba tare da gurfanarwa ba. Ya ƙalubalanci yadda aka ɗauki tsawon lokacin ana tsare ɗalibar har na tsawon sama da wata guda musamman da kuma yadda aka shigar da ƙorafin tuhuma ɗaya akanta mai alaƙa da wata wallafa a Soshiyal Mediya.

Ya bayyana cewa, abin da ake zargin Maryam da shi na iƙirarin da ta yi a kafar sada zumunta na zargin daraktan shiyya na EFCC da hannu a rashawa, har zuwa yanzu hukumar ba ta fitar da ainihin abin da sakamakon bincikensa ya nuna ba don tabbatarwa ko kore zargin nata.

Haka kuma, lauyan ya zargi EFCC da bayyana tuhumar da ake mata ana gab da gurfanar da ita ba tare da bai wa lauyoyinta damar kimtsawa ba domin su ba ta kariya da nema mata beli.

Akan haka ne Hikima ya yi kira ga shugaban lauyoyin na ƙasa da ya yi nazari kan al’amarin, yana mai gargaɗin cewa cigaba da jinkiri wajen yin shari’a kan al’amarin ka iya shafar kimar Nijeriya wajen bayar da haɗin kai ga biyayya ga hukunce-hukuncen ‘yancin ɗan-adam.

By Babaji

Leave a Reply