An fara fafata yaƙin neman zaɓen 2027

Spread the love

*’Yan takara sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar lumana

*Ya kamata kamfen ya zama gasa, ba yaƙi ba – Amupitan

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar Nijeriya na 2027 ya fara ne a hukumance ranar Laraba, 19 ga Agusta, kamar yadda jadawalin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta tanada ya nuna. Sai dai duk da fara wa’adin yaƙin neman zaɓen, manyan jam’iyyun siyasar ƙasar ba su nuna gaggawar fara gangamin neman ƙuri’u ba, yayin da wasu daga cikinsu ke ci gaba da shirye-shiryen kafa kwamitocin yaƙin neman zaɓe da tsara dabarunsu.

Rahotanni sun nuna cewa manyan jam’iyyun da suka haɗa da Jam’iyyar APC, Jam’iyyar NDC da ADC ba su shirya fara gangamin siyasa nan take ba. Haka kuma, ƙananan jam’iyyu na ci gaba da shirye-shiryen tunkarar tsawon wa’adin yaƙin neman zaɓen da zai kai kusan watanni biyar. Yaƙin neman kujerun Majalisar Dokokin ƙasa ma ya fara ne a ranar Laraba, kasancewar zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar za su gudana a rana guda. A wannan zaɓe, Shugaba Bola Ahmed Tinubu na APC zai nemi ƙarin wa’adi, yayin da Peter Obi na NDC, Atiku Abubakar na ADC da wasu ’yan takara 16 za su fafata da shi.

Wani babban jami’in ɗaya daga cikin manyan jam’iyyun siyasar ya bayyana cewa tsawon lokacin da aka ware wa yaƙin neman zaɓen na iya zama nauyi ga jam’iyyu.

“Ba mu shirya fita neman ƙuri’a tsawon watanni biyar ba. Akwai tsada, yana cin ƙarfi kuma yana da matuƙar wahala,” inji jami’in.

Ya zuwa yanzu, babu ɗaya daga cikin manyan jam’iyyun da ya bayyana cikakken tsarin ayyukan yaƙin neman zaɓensa ko kuma ya kafa kwamitin yaƙin neman zaɓe a hukumance.

Fara yaƙin neman zaɓen ya kasance mataki na shida cikin jadawalin ayyukan da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar.

Matakin ya yi daidai da Sashe na 98 (1) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya tanadi cewa kowace jam’iyya za ta fara yaƙin neman zaɓe kwanaki 150 kafin ranar zaɓe, kuma ta dakatar da shi sa’o’i 24 kafin ranar zaɓe.

Yaƙin neman zaɓen kujerun gwamna da na majalisun dokokin jihohi, waɗanda aka tsara gudanar da su a ranar 6 ga Fabrairu 2027, ana sa ran zai fara ranar 9 ga Satumba.

A wani ɓangare kuma, jam’iyyun siyasa suna da wa’adin zuwa 22 ga Agusta domin sauya duk wani ɗan takara da ya janye daga takara, bisa tanadin Sashe na 31 na Dokar Zaɓe.

INEC ta kuma ce jam’iyyu suna da wa’adin zuwa 29 ga Agusta domin gabatar da fom ɗin tantance ’yan takararsu, wato Forms 13A zuwa E, kamar yadda Sashe na 30(1) ya tanada.

Ana sa ran hukumar zaɓen za ta wallafa cikakken jerin ’yan takarar da aka amince da su ranar 12 ga Satumba, kamar yadda Sashe na 32 (1) na dokar ya tanada.

Wani mamba na Kwamitin Ayyuka na ƙasa (NWC) na ɗaya daga cikin manyan jam’iyyun adawa ya ce shugabannin jam’iyyar ba sa gaggawar fara yaƙin neman zaɓe. Ya ce jam’iyyar na da tsawon watanni biyar, don haka shugabanninta za su yi wani taro a ƙarshen watan domin tsara yadda za a gudanar da yakin neman zaɓen.

Haka kuma, wani ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin tutar APC ya ce tsawon lokacin yakin neman zaɓen na iya jefa ’yan siyasa cikin gajiya. “Watanni biyar na yaƙin neman zaɓe? Hakan zai yi mana nauyi matuƙa,” inji shi.

Sai dai Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na APC, Feliɗ Morka, ya bayyana cewa jam’iyyar na shirin fitar da cikakken tsarin yaƙin neman zaɓenta a faɗin ƙasar nan gaba cikin watan. Morka ya bayyana cewa ko da yake 19 ga Agusta ce ranar da INEC ta kayyade domin fara wa’adin yaƙin neman zaɓe, hakan ba yana nufin dole jam’iyyu su gudanar da gangami a wannan rana ba. Ya ce, abin da doka ta hana shi ne wata jam’iyya ta fara yakin neman zaɓe kafin ranar da INEC ta ƙayyade. A cewarsa, APC na son tsara dabarunta sosai tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki kafin ta fara gangamin neman ƙuri’a.

A nata ɓangaren, Shugaban Jam’iyyar PDP, Abdulrahman Mohammed, ya bayyana cewa jam’iyyar a shirye take domin tunkarar zaɓen. Ya ce PDP ta kasance jam’iyyar da ke da tsarin dimokuraɗiyya kuma tana da kasancewa a dukkan jihohin Nijeriya 36, da Babban Birnin Tarayya Abuja, da kuma ƙananan hukumomi 774. Mohammed ya ce, burin PDP shi ne samar da shugabanci nagari ga al’ummar Nijeriya.

Ita kuwa Jam’iyyar LP ta bayyana cewa za ta yi amfani da alaƙarta da Majalisar ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) da Majalisar ƙungiyoyin ƙwadago (TUC) wajen tattara magoya baya da ƙarfafa yaƙin neman zaɓenta daga matakin ƙasa.

Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na LP, Ken Asogwa, ya ce jam’iyyar ta tanadi ingantaccen tsarin ƙungiya, dimbin mambobi masu ƙwazo da ɗan takarar shugaban ƙasa da ta yi imanin yana da karɓuwa.

Asogwa ya ce babbar damar LP ita ce alaƙarta da ƙungiyoyin ƙwadago, domin NLC da TUC na daga cikin tsarin ƙungiyoyin da ke da alaƙa da jam’iyyar. Ya yi iƙirarin cewa babu wata jam’iyya a Nijeriya da za ta iya yin gogayya da LP wajen samun irin wannan babbar hanyar sadarwa ta ƙasa baki ɗaya, kasancewar ma’aikata da tsoffin ma’aikata suna zaune a kusan kowace rumfar zaɓe, gunduma, ƙaramar hukuma da al’umma. Ya ce shugabancin jam’iyyar na yanzu ya ƙuduri aniyar amfani da wannan ƙarfin ƙungiyoyin ƙwadago da tsarin jam’iyyar na matakin ƙasa wajen tallata ’yan takararta da manufofinta ga masu zaɓe.

Mista Asogwa ya kuma bayyana fatansa na cewa, INEC za ta wallafa sunayen ’yan takarar LP na gwamna da majalisun dokokin jihohi, yana mai cewa jam’iyyar ta cika wa’adin da hukumar ta gindaya na gabatar da sunayen ’yan takararta.

Yadda ’yan takara suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya:

’Yan takarar shugaban ƙasa da shugabannin jam’iyyun siyasa da za su fafata a zaɓen 2027 sun rattaba hannu kan Yarjejeniyar ƙasa ta Zaman Lafiya, inda suka yi alƙawarin gudanar da kamfen bisa muhimman manufofi, tare da yin watsi da tashin hankali, kalaman ƙiyayya, cin mutuncin abokan hamayya, yaɗa labaran ƙarya da kuma rura wutar rikicin ƙabilanci ko na addini.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Talata a Abuja, ƙarƙashin jagorancin Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa (NPC) tare da haɗin gwiwar Cibiyar Kukah, gabanin fara kamfen ɗin zaɓen 2027 a ranar Laraba.

Masu shirya taron sun ce yarjejeniyar ba wata takarda ce ta bikin rattaba hannu kawai ba, domin tana da tushe ne a cikin Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, Dokar Zaɓe, ƙa’idojin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da sauran dokokin da suka shafi tsarin zaɓe.

Manufar yarjejeniyar ita ce hana fafatawar neman ikon siyasa ta rikiɗe zuwa tashin hankali, tsoratarwa, yaɗa bayanan ƙarya da sauran abubuwan da ka iya raunana dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Sai dai rashin halartar wasu manyan ’yan takarar shugaban ƙasa, ciki har da ɗan takarar Jam’iyyar APC, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da ɗan takarar Jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya fito fili. An wakilci Tinubu a wajen taron ne da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume.

Daga cikin ’yan takarar shugaban ƙasa da suka halarci taron akwai ɗan takarar Jam’iyyar NDC, Peter Obi; ɗan takarar Jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo; da ɗan takarar Jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore. Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, shi ma ya halarci bikin.

Jim kaɗan kafin rattaɓa hannun, Peter Obi ya buƙaci ’yan Nijeriya su hukunta ’yan siyasar da suka karya yarjejeniyar ta hanyar kin zaɓensu a ranar zaɓe.

Da aka tambaye shi irin hukuncin da ya kamata a ɗauka kan ɗan takara ko jam’iyyar da ta karya yarjejeniyar, tsohon Gwamnan Jihar Anambra ya ce mafita ita ce masu zaɓe su ƙi ba su ƙuri’unsu.

Manajan Ayyukan Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa a Cibiyar Kukah, Asabe Ndaye, ta ce yarjejeniyar alƙawari ce da jam’iyyu da ’yan takara suka yi a gaban jama’a, kuma tana da goyon bayan dokokin ƙasa; ba takardar bikin siyasa kawai ba ce.

Ta ce yarjejeniyar na buƙatar shugabannin jam’iyyu, ’yan takara, masu magana da yawun kamfen, jami’ai da magoya baya su guji ƙirƙira, wallafawa, yaɗawa ko amincewa da labaran ƙarya da bayanan da aka karkatar da su domin tayar da hankali ko raunana sahihancin zaɓe.

Ndaye ta ce dokokin ƙasa sun tanadi hukunci kan laifukan da suka shafi tashin hankali, tsoratarwa, kalaman tunzura jama’a da kuma rarrabuwar kai ta fuskar ƙabila, addini ko wani ɓangare na al’umma.

Ta bayyana cewa tun kafuwar kwamitin, an taimaka wajen samar da yarjejeniyoyin zaman lafiya 31, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa zaman lafiyar dimokuraɗiyya.

Ya kamata kamfen ya zama gasa, ba yaƙi ba – Amupitan

Shugaban Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da ’yan takara da su mayar da yaƙin neman zaɓen 2027 zuwa “kasuwa ta ra’ayoyi da manufofi”, maimakon mayar da shi “filin yaƙi”.

Amupitan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja, yayin bikin rattaba hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta ƙasa ta farko da aka shirya gabanin babban zaɓen 2027. Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa, ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban ƙasa Janar Abdulsalami Abubakar, ne ya jagoranci shirya taron.

Da yake jawabi ga ’yan takarar shugaban ƙasa da shugabannin jam’iyyun siyasa, shugaban INEC ya ce yarjejeniyar da za a rattaba hannu a kanta ba takarda ce kawai ta al’ada ba, illa dai wata alƙawarin siyasa da zamantakewa tsakanin shugabanni da al’ummar Niueriya, wadda kuma doka da Kundin Tsarin Mulki suka kafa. Ya ce: “Takardar da kuke shirin sanya hannu a kanta ba takarda ce kawai ba. Alƙawari ce da kwangilar zamantakewa da al’ummar Nijeriya, kuma yarjejeniya ce mai ginshiƙin doka da Kundin Tsarin Mulki.”

Amupitan ya buƙaci shugabannin siyasa su zama abin koyi, yana mai cewa maganganunsu da halayensu kan yi tasiri kai tsaye ga magoya bayansu. Ya ce idan ’yan takarar shugaban ƙasa suka yi amfani da harshen zaman lafiya, magoya bayansu za su bi sawunsu, amma idan suka rura wutar rikici, magoya bayan ma za su iya mayar da hakan zuwa tashin hankali.

Shugaban INEC ya shawarci ’yan takara da su mayar da kamfen ɗinsu kan manufofi da hanyoyin magance matsalolin ƙasa, maimakon kai wa abokan hamayya hari ko mayar da hankali kan batutuwan da ba su shafi ci gaban ƙasa ba. Ya ce ya kamata ’yan siyasa su bayyana wa masu zaɓe abin da za su yi da kuma yadda za su cimma hakan, musamman a fannoni kamar tattalin arziki, tsaro da ilimi.

Ya ce: “Kamfen ɗin 2027 ya zama kasuwa ta ra’ayoyi, ba gidan wasan kwaikwayo na yaƙi ba.”

Amupitan ya kuma buƙaci ’yan siyasa su mutunta dokokin zaɓe da hukumomin da aka kafa domin gudanar da zaɓe, tare da yin suka mai ma’ana da gina ƙasa. Ya gargadi ’yan takara da magoya bayansu kan yin shelar nasara tun kafin sakamakon zaɓe ya fito ko yada bayanan da za su iya raunana amincewar jama’a ga hukumomin dimokuraɗiyya. Shugaban hukumar zaɓen ya kuma nuna damuwa kan yadda hanyoyin sadarwar zamani ke ƙara yin tasiri a harkokin zaɓe, yana mai gargaɗin ’yan siyasa da masu zaɓe kan haɗarin labaran ƙarya, yaɗa bayanan bogi da kuma katsalandan daga ƙasashen waje ta hanyar bayanai na zamani.

Farfesan shari’ar ya buƙaci dukkan jam’iyyun siyasa da ’yan takara su amince da tanade-tanaden yarjejeniyar zaman lafiyar tare da gudanar da kamfen cikin natsuwa da ɗaukar alhaki. Ya ce: “Mu yi gasa cikin mutunci, amma mu tuna cewa a ƙarshen wannan gasa, babu wanda zai yi nasara idan Nijeriya ba ta yi nasara ba.”

A bisa jadawalin INEC, za a fara yakin neman zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta ƙasa a ranar Laraba, 19 ga Agusta 2026, yayin da aka sanya ranar 16 ga Janairu 2027 domin gudanar da zaɓen. Amupitan ya kuma tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa INEC za ta kasance mai tsaka-tsaki a zaɓen 2027, yana mai jaddada cewa hukumar ba ta da ɗan takarar da take goyon baya ko wata jam’iyyar da ta fi so.

Ya ce: “Ina son in bayyana babu shakka cewa INEC ba ta da wata muradin ganin wani ya ci ko ya sha kaye a zaɓe, kuma ba ta fifita kowace jam’iyya ta siyasa. Abin da muke nema shi ne tsarin zaɓe mai bin doka, gaskiya, sahihanci da kuma haɗa kowa.”

Ya ƙara kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da aka yi wa rajista, ’yan takarar shugaban ƙasa da sauran ’yan takara da su ɗauki alƙawuran da ke cikin yarjejeniyar zaman lafiya da muhimmanci tare da aiwatar da su a aikace.

Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa ya fara gabatar da irin wannan yarjejeniya ne gabanin zaɓen shekarar 2015, a wani mataki na inganta zaman lafiya a lokacin zaɓe, sasanta rikicin siyasa da kuma ƙarfafa ’yan siyasa su amince da sakamakon zaɓe.

By ukarofi

Leave a Reply