Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu mata daga al’ummar Bin-Per da ke gundumar Kombun, ƙaramar hukumar Mangu a Jihar Filato, sun gudanar da zanga-zangar lumana kan kisan mutane 24 da wasu ’yan bindiga suka yi a yankin.
Matan sun ratsa cikin al’ummar rike da ganyaye a kawunansu, yayin da suke alhinin waɗanda aka kashe tare da kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa domin kare rayukan jama’a daga sake fuskantar hare-hare.
Zanga-zangar ta biyo bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai wa al’ummar cikin dare, inda rahotanni suka ce sun shiga gidaje tare da kashe mazauna yankin.
ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, Ladi Joshua, ta ce matan sun shiga cikin babban tashin hankali sakamakon rasa mazajensu, ’ya’yansu, ’yan uwansu da sauran ’yan al’umma.
A halin yanzu, an yi wa mutane 24 da aka kashe jana’izar bai ɗaya, yayin da wasu da suka jikkata ke karɓar magani a asibitoci.
Shugaban Mwaghavul Youth Movement, Kyesmang Jonathan, ya bayyana hakan yayin wani taron jana’izar waɗanda aka kashe.
Ya ce kawo yanzu an binne mutane 24, yayin da wasu daga cikin waɗanda suka samu raunuka ke ci gaba da karɓar magani.
Jonathan ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai cewa abin takaici ne da ke nuna irin haɗarin da al’ummomin yankin ke fuskanta. Ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa domin kare al’ummomin da ke cikin haɗari.
Ya kuma buƙaci hukumomin tsaro su gano, kama tare da gurfanar da waɗanda suka aikata kisan a gaban kotu.
A nasa ɓangaren, Sakataren Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na Jihar Filato, Jude Eli Dakur, ya bayyana harin a matsayin “mummuna, rashin hankali kuma abin da ba za a amince da shi ba.”
Dakur ya yi Allah-wadai da asarar rayuka da lalata gidaje, gonaki da sauran dukiyoyin jama’a.
Ya ce kashe mazauna yankin, musamman waɗanda aka farmaka yayin da suke barci a gidajensu, babban hari ne kan rayuwar ɗan Adam da bai kamata ya zama ruwan dare a Jihar Filato ba.
Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da ingantaccen bincike, gano tare da kama waɗanda suka aikata harin domin su fuskanci hukunci.
Dakur ya kuma buƙaci a ƙara tattara bayanan sirri da sanya ido a al’ummomin da ke cikin haɗari a Mangu da sauran sassan jihar.
Ya ce ya kamata a tura isassun jami’an tsaro zuwa wuraren da ke cikin haɗari tare da samar da tsarin gaggawar kai ɗauki domin ba da damar mayar da martani cikin sauri idan aka samu kiran neman agaji.
Dakur ya ƙara da cewa harin ya fi tayar da hankali saboda yadda matsalolin tsaro ke ci gaba da addabar al’ummomi a sassan Jihar Filato.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Filato da hukumomin tsaro da su ƙara haɗin gwiwa wajen inganta tsaro da dawo da kwarin gwiwar jama’a.
