Blueprint ta karrama Gwamnan Sakkwato kan shugabanci nagari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu Sakkwato, ya lashe kyautar lambar yabo ta Kamfanin Jaridun Blueprint ta 2025 kan Shugabanci nagari, Sabunta Cibiyoyi da kuma Ci-gaba Mai ɗorewa, wanda ya biyo bayan cimma nasarori wajen ƙarfafa cibiyoyin gwamnati da gyare-gyare masu kyawawan tasiri a sassan jihar da aka samu a ƙarƙashin gwamnatinsa.

Kwamishinan Ƙirƙira da Tattalin Dijital, Hon. Bashar Umar Kwabo ne ya wakilci gwamnan a taron Karramawar ta Blueprint Newspapers Limited, wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja a ranar Talata.

A yayin gabatar masa da kyautar, jaridar ta bayyana rawar da gwamnan ya taka wajen dawo da ƙwarin-gwiwa a gwamnati da ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da adalci, inganci da ci-gaba mai ɗorewa tun bayan hawa kujerar mulkin jihar a watan Mayun 2023.

Hakan na zuwa ne bayan da gwamnan ya samu lambar yabo ta Jaridar Sun ta 2024 kan sabunta zuba jari a ƙarƙashin tsarin ajanda tara (9-Point Smart Agenda) na gwamnatinsa.

Gwamna Aliyu dai akanta kuma jami’in lamuran gudanarwa ne, wanda ya taɓa riƙe muƙaman kwamishina da mataimakin gwamna a Sakkwato. Sannan shi ne babban sakataren farko na Asusun Tallafa wa Harkokin ‘Yan Sandan Nijeriya.

Gwamnatinsa ta duƙufa wajen gina titina, samar da ruwa, inganta cibiyoyin lafiya, ilimi da ci-gaban harkar tattali a jihar. Kazalika, ta ɗauki mutum 3,000 aikin gwamnati don inganta harkokinta a jihar, da kuma zuba jari a tsaro ciki har da samar da hukumar tsaron al’ummar jihar Sakkwato da bunƙasa walwalar jami’an tsaro.

Har ila yau, don ƙarfafa harkar lafiya daga tushe, gwamnatin ta amince da ɗaukar ma’aikatan lafiya 2,440, wato guda 10 daga kowacce gunduma daga gundumomi 244 na faɗin jihar.

Sauran waɗanda aka karrama a taron tare da gwamnan sun haɗa da gwamnonin Enugu, Peter Mbah; Dauda Lawal na Zamfara; Agbu Kefas na Taraba; Jigawa, Umar Namadi; da Bassey Otu na Kuros-Riba; da kuma Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso.

Taron ya kuma samu halartar tsohon gwamnan Jihar Zamfara Sanata Abdul’aziz Yari; Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda; Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris da dai sauransu.

By Babaji

Leave a Reply