Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ana fargabar mutuwar mutane sama da 40 bayan wani kwale-kwale ɗauke da manoma da ma’aikatan gona ya kife a garin Gorau, da ke ƙaramar Hukumar Goronyo a jihar Sakkwato.
Rahotanni sun ce mutanen na kan hanyarsu ne zuwa gonakin shinkafa domin gudanar da ayyukan noma, musamman girbin amfanin gona, lokacin da kwale-kwalen ya kife jim kaɗan bayan tashi daga bakin ruwa.
Lamarin ya jefa fasinjojin da dama cikin ruwa, inda wasu suka nutse, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto da neman waɗanda suka ɓace.
Shaidu sun bayyana cewa sama da mutane 70 ne ake zargin suna cikin kwale-kwalen a lokacin da hatsarin ya faru, lamarin da ya ƙara tayar da fargabar cewa adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa.
Rahotanni sun ce mafi yawan mutanen da ke cikin jirgin yara ne ‘yan tsakanin shekaru 10 zuwa 15, waɗanda suka bi iyayensu da sauran ma’aikatan gona domin zuwa aikin girbin shinkafa.
An kuma ruwaito cewa shugaban ƙauyen na daga cikin mutanen da ke cikin jirgin, amma an yi nasarar ceto shi tare da wasu mutane biyar.
Wani ɗan jarida, Sharhabilu Yahuza Kiliya, wanda ya kasance a wurin da hatsarin ya faru, ya ce kawo yanzu an gano gawarwakin mutane kusan 40, yayin da mutane shida, ciki har da shugaban ƙauyen, suka tsira.
“Ya zuwa yanzu, mun gano gawarwaki kusan 40, yayin da aka ceto mutane shida, ciki har da shugaban kauyen. Aikin ceto har yanzu yana ci gaba,” inji Kiliya.
Ya ce, mutanen da ke cikin jirgin sun haɗa da masu gonaki da kuma ma’aikatan da aka ɗauka domin taimakawa wajen girbin shinkafar.
Kiliya ya bayyana cewa kwale-kwalen ya kife ne jim kaɗan bayan ya taso, lamarin da ya sa wasu fasinjoji suka maƙale a cikin ruwa, yayin da wasu kuma ruwa ya kwashe su.
Ya ce masu aikin ceto na cikin al’umma, musamman kwararrun masu nutsewa cikin ruwa, na ci gaba da bincike domin gano mutanen da har yanzu ba a san inda suke ba tare da kuma kwaso gawarwakin da aka gano.
Mazauna yankin na ci gaba da haɗa kai wajen aikin ceto, yayin da hukumomi da al’ummar garin ke ƙoƙarin tabbatar da ainihin adadin mutanen da ke cikin jirgin da kuma gano waɗanda har yanzu suka ɓace.
Hatsarin ya haifar da matuƙar damuwa a yankin, musamman ganin rahotannin cewa yara da dama ne ke cikin jirgin.
Lamarin ya kuma sake jawo hankali kan matsalar tsaron hanyoyin ruwa da manoma ke amfani da su wajen isa gonakinsu, musamman a lokacin da ake gudanar da ayyukan noma.
