DSS ta yi gargaɗin ‘yan ta’adda na shirin kai farmaki manyan makarantu a Sakkwato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) reshen Jihar Sakkwato, ta nuna damuwa kan wani rahoton leƙen asiri da ke nuna cewa ‘yan ta’adda da ƙungiyoyin ‘yan bindiga na shirin ƙaddamar da wasu hare-hare a manyan makarantu da ke faɗin jihar, inda ɗalibai, malamai, sauran ma’aikata da iyalansu suna cikin halin haɗarin a yi garkuwa da su.

DSS ta fitar da saƙon ankararwar ne a wata takarda mai ɗauke da 18 ga Agusta, 2026, wadda ta gabatar ga gwamnatin Jihar Sakkwato kuma da aka sanya wa hannu a madadin daraktan tsaron jihar.

A saƙon, mai taken “Planned Attack on Tertiary Institutions by Terrorists and Bandit Gangs”, DSS ta ce rahoton leƙen asiri da ta samu ya nuna cewa ƙungiyoyin ‘yan bindiga sun fara sauya salo daga fakwan makarantun firamare da sakandare zuwa kan jami’o’i da wasu manyan makarantu.

Hukumar ta bayyana hakan a matsayin babbar barazana ga fannin ilimi, inda ta ce manyan makarantu suna da jama’a da dama da suka haɗa da ɗalibai da malamai da sauran ma’aikata har ma da iyalansu.

A cewar DSS, muddin aka samu nasara a wani farmaki, to hakan zai haifar da ƙalubale ga ba iya ɗaiɗaikun mutane ba, har ma ga harkokin karatu da sanya fargaba acikin mazauna gami da karaya ga ƙoƙarin gwamnati na bai wa cibiyoyin ilimi kariya daga ɓangaren al’umma.

Kazalika, hukumar ta yi gargaɗin cewa hari akan manyan makarantu ka iya ɓata wa Nijeriya suna a idon duniya da ƙamarin ƙalubalen tsaro da tuni yake tasiri a harkar ilimi a sassa da dama na ƙasar. Don haka DSS ta ke kira ga gwamnatin jihar da hukumomin tsaro da su ƙarfafa tsaro a yankunan jami’o’i da wasu manyan makarantu da ke faɗin jihar.

By Babaji

Leave a Reply