‘Davido aka so halakawa’, inji ‘yan sanda kan harin ayarin motocin Gwamnan Osun

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shahararren Mawaƙin Nijeriya, David Adeleke da aka fi sani da Davido, shi ne wanda aka nufa yayin da aka farmaki ayarin motocin Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a cewar rundunar ‘yan sandan jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaron da ke tsare gwamnan sun yi musayar wuta da maharan a lokacin da ya kai wa Ataoja na Osogbo ziyara a ranar Laraba. Gwamnan ya kai ziyarar ne jim-kaɗan bayan karɓar shaidar zama gwamna a ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ke jihar bayan sake zaɓarsa.

Davido, wanda ɗa ne a gurin Adeleke, yana daga cikin waɗanda suka yi masa rakiya zuwa ofishin INEC da fadar mai martaban tare da ‘ya’yansa.

Wasu mazauna yankin Oja Oba da ke Osogbo, sun ce an ɗauki tsawon mintina 15 ana jin ƙarar harbin bindiga yayin ba-takashin, lamarin da ya jefa su cikin firgici.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abiodun Ojelabi ya ce bincike ya nuna cewa, ana zargin mambobin ƙungiyar “Eye Confraternity” suna neman rayuwar Davido.

A cewarsa, an harbe wani dattijo mai shekaru 60, Tajudeen Yusuf a yayin arangamar a yankin Itaolokan a Osogbo.

Ojelabi ya ƙara da cewa, rundunar tana aiki tuƙuru wajen ganin ta gano tare da kamo dukkan waɗanda ake zargin da gurfanar da su domin su fuskanci hukuncin doka.

By Babaji

Leave a Reply