Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Aisha Adam, wacce aka fi sani da Aishacool, na daga cikin matasan marubuta mata da tauraron su ke haskawa a duniyar rubutun Hausa. Ta rubuta littattafai da yawansu ya zarta goma, waɗanda suka taɓo ɓangarori daban-daban da suka shafi zamantankewar al’umma. Marubuciyar ta kasance Ma’aikaciyar jinya ce kuma mai sha’awar aikin jarida. Ta shaidawa wakilin Manhaja Blueprint, Abba Abubakar Yakubu cewa abin da ya fi bata sha’awa a harkar rubutun adabi shi ne yadda rubutun da take yi yake tasiri a rayuwar wasu. A yi karatu lafiya.
MANHAJA: Ina so ki gabatar mana da kan ki.
AISHA COOL: Sunana Aisha Adam. Ni marubuciya ce. Ina rubutun littattafan Hausa na onlayin. Sannan ina taɓa kasuwanci, kuma ni ma’aikaciyar lafiya ce. A lokaci guda kuma ni ɗalibar aikin jarida ce.
Ki gaya mana tarihin rayuwarki?
Ni haifaffiyar garin Kano ce, daga ƙaramar Hukumar Gwale. Na yi karatuna a matakin firamare, sakandire, har zuwa matakin diploma a makarantar kwalejin kiwon lafiya duk a nan Kano. A ɓangaren karatun addini kuwa na yi karatun Muhammadiya har zuwa saukar Alƙur’ani.
Ko za ki gaya mana yadda aka yi ki ka samu sunan Cool?
Sunan Cool na same shi ne, tun a farkon fara rubutuna, zan iya cewa masu karatu ne suka saka mini wannan sunan. A lokacin ina rubuta wani littafina mai suna Abdujalal, sai sukan ce ina cooling ɗin su da soyayyar cikin labarin.
Ba ni labari kan irin rayuwar da ki ka taso da ita lokacin ƙuruciyarki, da irin tarbiyyar da ki ka samu?
Alhamdulillah! Mun godewa Allah Subhanu Wa Ta’ala. Gaskiya an mori tarbiyya daga gurin jajirtattun iyaye. Na taso da tun ina yarinya da yawan tambayoyi, da samun nishaɗi ta hanyar karance-karance. Sai dai mahaifiyata ta yi ƙoƙari sosai lokacin da nake ƙadamin yin tambayoyin da suka tsallake shekaruna. Abu ɗaya ne duk dabarun ta ba ta iya raba ni da shi ba, shi ne son karance-karance da ƙananan shekaruna.
Mene ne alaƙarki da rubuce-rubuce da karatu, kina samun damar yin karance-karance?
E, kamar yadda na faɗa a baya, kasancewata ‘yar fari na samu kulawa sosai a kan karatu. Tun ina aji na farko zuwa na biyu a firamare na iya haɗa baƙi, komai aka nuna min zan iya karanta shi tas. Don haka duk abin da na ci karo da shi burina na karanta shi komai tsaurinsa, ko da ban iya furta shi yadda ya kamata ba. Karatu ya yi tasiri sosai a rayuwata.
Wanne littafi ki ka taɓa karantawa wanda ya tsaya miki a rai, kuma har yanzu kin kasa mantawa da shi?
Akwai littafin ‘Sanin Gaibu’, naso littafin nan sosai da sosai. Labari ne kan wani tubabben ɗan fashi da wata lauya. A gaskiya ina son na ga ana zuwa da abubuwa na musamman a littattafai, ba lallai sai labarin soyayya ba. Zan iya cewa labaran nishaɗi ko na ƙirji ɗarɗar, sun fi jan hankalina.
Kawo yanzu kina ganin kin karanta littattafai sun kai nawa?
Ba zan iya cewa ga adadin litattafan da na karanta ba, amma na karanta littattafai da yawa.
Har yanzu kina samun lokacin yin karatu? Kuma wanne littafi ki ke karantawa a yanzu?
Gaskiya a yanzu, ba na iya yin dogon karatu sosai, saboda yadda ayyuka suke yi mini yawa. Babu littafin da nake karantawa yanzu, amma akwai wadanda nake fatan karantawa idan na samu sarari.
Daga wanne lokaci ki ka fara tunanin rubuta littafi na kanki?
Na fara rubutun adabi tun a shekarar 2019. Na daɗe ina tara labarai da yawa a kaina, ban san ta ina zan fara ba. Saboda fargabar ka rubuta ka buga, doguwar hanya ce. Kuma ba na tunanin zan samu goyon baya a lokacin saboda ina karatu. Bayan zuwan marubutan onlayin sai na ji lokaci ya yi da ya kamata nima na ba da gudunmawata ga kyautatuwar rayuwar al’umma.
Kawo yanzu kin rubuta littattafai sun kai nawa? Kawo mana sunayensu da bitar wasu daga ciki a taƙaice.
Na rubuta littattafai goma sha ɗaya. Akwai, ‘Abduljalal’, ‘Wata Kissar Sai Mata’,
‘Aƙidata’, ‘Gaba Da Gabanta’, ‘Wuta A Masaƙa’, ‘Rudin ƙuruciya’, ‘Cutarwa’, ‘ƙanwar Maza’, ‘ƙarfe A Wuta’, ‘Buzu’, da kuma ‘Sara Da Sassaƙa’.
Shi littafin ‘Sara Da Sassaƙa’, yana ɗauke ne da wani labari da yake magana a kan ƙalubalen tsaro da siyasa a cikin al’umma.
Shi kuma littafin ‘ƙarfe A Wuta’, yana magana ne akan illolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, harkar daba da kuma bangar siyasa.
Littafin ‘Buzu’, kuma labari ne na almara, amma yana da alaƙa da magungunan gargajiya, harkar bori, aljanu, da makamantansu.
Kin taɓa wallafa wani daga cikin littattafan da ki ka rubuta?
A’a ban taɓa wallafa ko ɗaya ba tukunna, amma ina da niyyar haka nan gaba in sha Allahu.
Kawo yanzu wanne littafin ki ke rubutawa, kuma a wanne matakin ki ke?
A yanzu ina rubuta littafin ‘Sara Da Sassaƙa’ ne. Na kammala littafi na farko, ina kan rubuta na biyu. Kamar yadda na faɗa a baya, rubutu ne akan halin da muke ciki na rashin tsaro.
Kina ganin mene ne ya bambanta ki da sauran marubuta da ke ƙoƙari a fagen adabin Hausa?
To, Alhamdulilh. Abin da na sani shi ne, rago ba ya zama marubuci, sannan kowane marubuci ɗan baiwa ne na musamman, kowa akwai inda ya fi ƙwarewa.
Ni dai kowanne ɓangare na ɗauka zan iya rubutu a kai, sannan kaf littattafai na goma sha ɗaya ɗin nan, kowanne jigonsa mai kyau ne. Alhamdulilh!
A ina ki ke samun jigon da ki ke rubuta littattafan da ki ke yi?
Ina samo jigo ne a cikin rayuwar al’umma. Ba abin mamaki ba ne, a hirar nan da muka yi da kai na samu jigon yin rubutu. Sai dai na fi ɗaukar jigona daga abubuwa masu muhimmanci da al’umma suka fi buƙata.
A wanne yanayi ki ka fi jin daɗin rubutu?
Na fi jin daɗin rubutu, a yanayin dare, kamar abin da ya kama daga bayan sha biyun dare, musamman kuma idan ya zamana bana jin yunwa, ko akwai abin ciye-ciye a kusa da ni.
Tsawon wanne lokaci ki ke ɗauka kafin ki kammala rubutun littafi?
E, wannan kuma ya danganta. Ni da yake ina cikin marubutan da suke rubutu suna wallafawa ne. Ina wata huɗu har shida ina rubutu, gwargwadon tsayin da labarin ke da shi.
Wanne littafinki ne ya fi tsayi, kuma wanne ne ya fi gajarta?
‘Wata Kissar Sai Mata’, shi ne littafin da ya fi gajarta. Amma kuma labarin ‘Buzu’ ya fi kowanne tsayi.
Wanne abu ne ya fi sa ki nishaɗi a lokacin da ba kya rubutu?
Kallon finafinan ƙetare, da sauraron ƙasidu.
Yaya ki ke amfani da shafukan sada zumunta wajen yaɗa rubuce-rubucenki?
E, na kan yi gajeren sharhi, a kan litattafana lokaci zuwa lokaci. Sannan ina bibiyar ra’ayoyin makarantana ta yadda suke jin daɗin rubuce-rubucen da nake yi.
Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?
Zakaran da Allah Ya nufa da cara…
Na gode.
Nima na gode.
