
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Filato, ta ce ta kama wanda ke zargi da kitsa mummunan harin ranar Talata da aka ƙaddamar a ƙauyen Bimper da ke Gundumar Kombun ta Ƙaramar Hukumar Mangu.
Rahotanni sun ce, harin ya yi ajalin kimanin mutane 25 yayin da jikkata wasu huɗu sakamakon raunuka a farmakin safiyar. Wannan shi ne karo na uku da aka ƙaddamar da harin ‘yan ta’adda acikin mako guda a Mangu.
Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Alfred Alabo ne ya tabbatar da kamen ga gidan talabijin na Channels, inda ya ce a yanzu haka wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda kuma ana kyautata zaton shi ne wanda ya kitsa mummunan harin.
A cewarsa bincike kan al’amarin na cigaba da gudana, yayin da jami’an tsaro suka ƙarfafa ƙoƙarinsu na farauto sauran maharan da suka tsere bayan harin domin gurfanar da su don su fuskanci hukuncin da doka ta tanada.
Harin na kwanan nan ya ƙara jefa al’umma cikin fargaba bayan jerin hare-hare da aka ƙaddamar a ƙaramar hukumar a ‘yan kwanakin nan. Majiyoyin yankin sun ce an harbi mutum guda a harin da ya gabata kafin wannan.
Akan haka ne mazauna yankin suke kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙarfafa matakan tsaron a ƙauyuka masu fuskantar barazanar hare-hare domin su samu kariya daga farmakin da ake yawan ƙaddamarwa akansu tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.
