Me ya sa ake yawan mantawa da ƙafa a kwalliya?

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Akwai abubuwan da mutum kan yi wa kansa ba tare da ya ɗauke su a matsayin wani nau’in kulawa ta musamman ba. Wanke fuska, shafa mai, gyaran gashi, tsaftace farce da neman kayan kwalliya masu kyau duk suna daga cikin abubuwan da mutane da dama suka saba yi domin su kasance cikin tsari.

Amma idan aka tambayi mutum yadda yake kula da ƙafafunsa, akwai yiwuwar amsar ta zama daban. Wataƙila ya tuna da lokacin da zai yi pedicure, ya shafa mai ko ya gyara farcen ƙafa. Amma kulawar kafa ta fi haka nisa.

Domin kafin takalmi ya yi kyau a ƙafa, kafin a yi wa farce ado, kafin a yi wa ƙafar kowane irin kwalliya, akwai wata muhimmiyar tambaya da ya kamata a fara yi: shin ƙafar tana cikin koshin lafiya?

ƙafa na daga cikin sassan jikin da mutum ke amfani da su kusan kowane lokaci, amma ba kasafai ake ba su irin kulawar da ake bai wa fuska ko hannu ba.

Ita ce ke ɗaukar nauyin jiki yayin da mutum yake tsaye kamar yadda muka bayyana a darasin baya, tana taimaka masa wajen tafiya, gudu, hawa matakala da gudanar da ayyukan yau da kullum.

Duk da wannan muhimmiyar rawa, mutane da dama ba sa kula da ita sai lokacin da matsala ta bayyana.

Fashewar diddige, bushewar fata, ciwon farce, kaikayi, wari, kumburi ko wani canji da ba a saba gani ba na iya zama abubuwan da mutum ya fara lura da su ne bayan sun daɗe suna faruwa.

A nan ne kula da kafa ke daina zama batun kwalliya kawai, domin kyakkyawar ƙafa ba iya launinta ko haskenta kawai ba ne.

Idan aka ce “kyakkyawar ƙafa”, abu na farko da kan zo wa mutum a rai shi ne farce mai kyau, fata mai laushi ko takalmi mai kyau. Amma kyawu na gaske yana da alaƙa da lafiyar abin da ake gani.

Fatar kafa mai tsafta, farce da ake kula da shi yadda ya kamata, da kuma ƙafar da ba ta fama da wata matsala da aka yi watsi da ita, duk suna daga cikin abin da ke sa ƙafa ta kasance cikin yanayi mai kyau.

Saboda haka, kwalliyar ƙafa ba tana fara wa da abin da za a gani kawai ba. Ya kamata ta fara da abin da zai tabbatar da cewa ƙafar tana cikin yanayi mai kyau.

Daga ƙarshe, yana da matuƙar muhimmanci mu canza irin kallon da muke yi wa gyaran ƙafa da kuma yadda muka ɗauke ta ta fuskar muhimmanci. 

Domin ƙafa ba ta buƙatar a tuna da ita ne kawai lokacin da za a saka takalmi mai kyau ko a yi wani biki. Tana buƙatar kulawa tun kafin matsala ta bayyana.

Wanke ta, busar da ita yadda ya kamata, kula da fatarta, gyara farce cikin tsafta, zaɓar takalmin da ya dace da ita da kuma lura da duk wani sabon canji da ya bayyana, duk suna cikin kulawar da za a iya yi wa ƙafa.

By ukarofi