Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jama’a daga ɓangarori daban daban na ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina na ci gaba da yin tururuwa zuwa gidan dan takarar gwamnan jihar ta Katsina ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Sanata Ahmad Babba Kaita domin yi ma shi barka da dawowa daga asibiti, da yi masa fatan alheri.
Haka zalika ‘yan uwa, dangi da tsaffin ‘yan ajin shi, sanatan da abokan arziki su kai masa ziyarar dubiya da fatan Allah bashi ƙwarin gwiwa ya cigaba da abubbuwan alheri kamar yadda ya aiwatar lokacin yana sanata shiyyar Daura.
Sanarwa daga jami’in hulɗa da jama’a na ɗan takarar Ahmed Abubakar ya bayyana cewa mutanen sun ta tofa albarkacin bakin su kan abubbuwan alheri da santanan ya aiwatar da ayyuka da suka haɗa da gina makarantu, ajujuwa, asibitoci, samar da ruwan sha, taimakawa ‘yan kasuwa, sama wa yara ayyuka a matakai daban daban a ma’aikatun gwamnatin taraiya da sauran hanyoyin walwala da dogaro da kai waɗanda ya cimma a dukkan faɗin jihar.
Sun kuma tabbatar da cewa, tallata ɗan takarar shugaban ƙasa da ɗan takarar gwamna na ADC a jihar Katsina ba za ta yi wuya ba la’akari da abubuwan da suka yi ko suka kawo na ci gaba a Najeriya da jihar Katsina.
Shi ma a na shi bayanan, ɗan takarar gwamnan, Sanata Ahmad Babba Kaita ya nuna godiya da jin daɗin matuƙa da irin karamcin da ake nuna ma shi daga ciki da wajen jam’iyyar ta ADC.
Ya kuma yi godiya ga jama’ar jihar da addu’o’i da goyon bayan da ake ba shi, ya kuma tabbatar da cewa, da ikon Allah, addu’ar al’umma da neman samun sauƙi da kawo sauyi mai ma’ana ADC za ta kafa gwamnati daga sama har ƙasa a zaɓukan 2027.
