Gwamnan Zamfara ya lashe kyautar gwarzon gwamna na Blueprint yayin da manyan jami’an gwamnati suka tafka muhawara kan tsaro da zaɓen 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamna Dauda na Jihar Zamfara ya samu kyautar lambar yabo ta Jaridar Blueprint ta 2026 kuma ta Gwarzon Gwamna mafi Ƙwarewa wajen Gudanar da Kuɗaɗen Al’umma da Tsare Gaskiya da Adalci, inda yake ƙoƙarin ganin gwamnatinsa ta ceto tare da sake gina Zamfara domin amfanin al’umma.

Dauda Lawal ya karɓi wannan kyauta ne a ranar Talata, 18 ga Agusta yayin taron Karramawa na Kamfanin Jaridun Blueprint na Shekara-Shekara, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre da ke Abuja, inda jagororin siyasa, ‘yan difulomasiyya, ƙungiyoyin al’umma, masana da sauran masu ruwa da tsaki suka taru domin tattauna muhimman al’amuran da suka shafi tabbatar da zaman lafiya da zaɓe na gaskiya a Nijeriya gabanin zaɓen 2027.

Taken taron na wannan shekarar dai shi ne “Security Challenges and Integrity of Nigeria’s 2027 Elections”, wato Ƙalubalen Tsaro da Kare Martabar Zaɓukan Nijeriya na 2027.

Da yake karɓar kyautar, Gwamna Lawal ya bayyana godiyarsa ga hukumar gudanarwar Jaridun Blueprint, sannan ya ci alwashin cewa gwamnatinsa za ta ƙara hoɓɓasa wajen samar da ababen more rayuwa a Zamfara domin ci-gaban al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.

Ya ce, “Wannan kyauta alama ce kan cewa gidajen jarida da ‘yan Nijeriya da ke wajen Zamfara suna shaida ƙoƙarin da gwamnatina take sanyawa wajen kai Zamfara gaci”.

A cewarsa, a tsawon shekaru uku na gwamnatinsa, sun cimma nasarori a fannonin tsaro, ilimi, lafiya, tattali, inganta ɗan-adam, ababen more rayuwa da dai sauransu, yana mai cewa sun cimma haka ne saboda gwamnatinsu ta tsayar da gaskiya da adalci ce.

A nasa ɓangaren, Kamfanin Blueprint ya ce an zaɓi gwamnan ne bisa fintinkau da ya yi acikin takwarorinsa wajen gudanar da dukiyar al’umma, tsare gaskiya wajen gudanar da lamuran kasafi da ƙoƙarin tafiyar da shugabancin Zamfara bisa gaskiya da adalci.

Darakta-Manaja na kamfanin jaridun, Salisu Umar ya ce Gwamna Lawa “na wakiltar cika alƙawarin ƙwarewa da hidimar al’umma”, wanda ƙwarewarsa a harkokin difulomasiyya, banki da tsare-tsare sun taimaka matuƙa wajen fahimtarsa ga shugabanci, gudanarwar kuɗi da jagorancin cibiya.

A nasa jawabin, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris ya jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta ƙarfafa lamuran tsaro da yaɗa labarai domin muhimmancinsu a zaman lafiya, gaskiya da adalci a zaɓukan 2027.

Haka kuma, ya yaba wa Blueprint bisa cigaba da ɗaukar nauyin taron shekara-shekaran, wanda ya bayyana a matsayin fagen haɗa masana harkokin tsare-tsare, ƙwararru, malamai, ‘yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki don tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ƙasa.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da: “Governor of Zamfara State, Dauda Lawal; Governor of Sokoto State, Ahmad Aliyu, represented by the Commissioner for Innovation and Digital Economy, Hon. Bashar Umar Kwabo; Governor of Cross River State, Senator Bassey Edet Otu, represented by his aide, Emmanuel Ogbeche; Governor of Enugu State, Peter Ndubuisi Mbah, represented by the Deputy Governor, Mr. Ifeanyi Ossai; and Governor of Taraba State, Agbu Kefas, represented by the Commissioner for Information, Barr. Zainab Jalingo”, kamar yadda NewsPointNigeria ta wallafa.

Haka kuma, akwai tsohon gwamnan Jihar Neja, “Senator Dr. Abubakar Sani Bello; former Governor of Bauchi State, Muhammad Abdullahi Abubakar, SAN; the Honourable Minister of Art, Culture, Tourism and Creative Economy, Hannatu Musawa; the Honourable Minister of Steel Development, Prince Shuaibu Abubakar Audu; Special Adviser to the President on Information and Strategy, Mr. Bayo Onanuga; National Chairman of the All Progressives Congress, Professor Nentawe Yilwatda; Director-General of Voice of Nigeria, Malam Jibrin Baba Ndace; Executive Secretary of the Nigerian Press Council, Nze Dili Ezughah; and Director-General of the Advertising Regulatory Council of Nigeria, Dr. Olalekan Fadolapo”, da dai sauran masu alfarma.

By Babaji

Leave a Reply