‘Yan bindiga sun halaka sufeton ‘yan sanda da wasu huɗu a sabon harin Adamawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu ‘yan bindiga sun halaka sufeton hukumar ‘yan sanda da wasu mutane huɗu a yayin wani hari da suka ƙaddamar a ƙauyen Gaya Dlang da ke Gundumar Kuva Gaya a Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa.

Al’amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Litinin, wanda kuma shi ne mummunan hari na biyu da aka samu cikin wata guda, kuma a haifar da fargaba acikin al’umma bisa hare-haren ‘yan bindiga.

Kakakin Runndunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahya-Nguroje ne ya sanar da haka yayin ganawa da wakilin gidan talabijin na Channels a hedikwatar hukumar da ke Yola.

A cewar rahotanni, maharan, yayin da suka afka wa ƙauyen, sun cinna wa gidaje da dama wuta da sace wasu kayayyakin abinci kafin suka tsere daga yankin. A lokacin harin, sun halaka wani sufeto da ke aiki a Kuva Gaya da wasu mutane huɗu.

Wannan na zuwa ne ƙasa da wata guda da wasu ‘yan ta’adda suka kai farmaki a ƙauyen Zah da ke Gundumar Yadul, harin da a cewar majiyoyi ya yi ajalin mutane biyar ciki har da jami’in tsaron gandun daji.

Nguroje ya ce, an tura jami’an tsaro ciki har da sojoji zuwa yankin Gaya Dlang domin ba wa ƙauyen kariya da kuma duba ainihin matakin ɓarnar da harin na kwanan nan ya yi.

Haka kuma, wasu mazauna yankin sun jikkata yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga harin ‘yan ta’addan, inda tuni aka garzaya da su Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Hong domin ba su kulawa. Sannan, tuni aka kai gawarwakin mamatan da harin ya shafa zuwa gidan ajiyar gawa da ke babban asibitin.

Kakakin ya kuma tabbatar wa al’umma cewa sun yi ƙoƙarin dawo da walwala a yankin bayan tura ƙarin wasu jami’ai zuwa yankin, yana mai cewa ana gudanar da bincike don gano masu hannu a harin da kuma gurfanar da su a gaban doka.

By Babaji

Leave a Reply