Iƙirarin ASUU cewa sama da lakcarori 200 sun yi murabus a KASU ba gaskiya ba ne, inji VC Farfesa Musa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), Farfesa Abdullahi Musa, ya yi watsi da iƙirarin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i rushen jami’ar (ASUU-KASU) na cewa sama da malamai 200 sun ajiye aikinsu kan rashin kyawun yanayin aiki, yana mai bayyana zargin a matsayin abin ruɗarwa da bai yi kama da haƙiƙanin al’amari ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan faɗi-in-faɗa ta samo asli ne bayan wani taron manema labarai da ASUU-KASU ta kira, inda ta yi zargin sama da farfesoshi da lakcarori 200 sun bar aiki da jami’ar bisa rashin kyawun yanayin aiki da gazawar cika alƙawarin aiwatar da yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU ta 2025.

A wata takarda da Farfesa Abdullahi Musa (VC) ya fitar a ranar Talata, ya ce iƙirarin bai yi daidai da ainihin hali da ake ciki ba a jami’ar, yayin da take cigaba da samun nasarori a harkar karatu, bincike da dai sauransu, waɗanda a cewar hukumar gudanarwarta, hakan na nuna za ta iya ci-gaba da riƙe manyan masana don cigaba da aiki da ita.

Daga bisani ƙungiyar ta ba wa hukumomi masu ruwa da tsaki wa’adin mako biyu domin a warware buƙatun mambobinta ko kuma ta tsunduma a yajin aiki.

Saidai, a nata ɓangaren hukumar gudanarwar KASU ta ce samuwar yanayin aiki a wurare daban-daban ga malaman da sauran ma’aikata a jami’o’i daban-daban a lokaci guda abu ne sanannen a tsarin gudanar da jami’a a matakin duniya, don haka kada a fassara hakan da rashin kyawun yanayin aiki.

Akan haka ne hukumar ta yi kira ga ASUU-KASU da ta riƙa gabatar da haƙiƙanin halin da ake ciki tare da ƙauce wa kalaman da za su iya haifar wa ɗalibai, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki shiga halin damuwa kan abin da ba haka yake ba. A cewar jami’ar, nasarori da ta samu a kwanan nan a karatu da bincike shaida ce kan cewa za ta iya janyo ra’ayoyi da riƙe manyan masana a fagen ilimi.

KASU ta kuma bayar da misalai na malamanta da suka yi fice duniya a fannin bincike, waɗanda suka haɗa da “Professor Ibrahim Inuwa Yahaya of the Department of Chemistry, Dr Daniel Yahaya Shagaiya of the Department of Mathematics and Dr Abdullahi Yusuf Zuntu of the Department of Physics”, waɗanda suna cikin gogaggun masana kimiyya na duniya.

Kazalika, ta ce gwamnatin jihar Kaduna ta zuba jarin sama da Naira miliyan 290 don ci-gaban shirye-shiryen harkokin karatu guda 90 da kuma tantance su.

By Babaji

Leave a Reply