Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA) ta kai ziyarar gani da ido zuwa ƙaramar hukumar Kankia domin tantance ɓarnar da ambaliyar ruwa ta haddasa.
Ziyarar ta gudana ne bisa umarnin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, domin duba irin asarar da aka samu tare da jajanta wa al’ummomin da iftila’in ya shafa.
Shugabar SEMA, Hajiya Binta Hussaini Dan-Gani, ta ce manufar ziyarar ita ce jajanta wa waɗanda abin ya shafa da kuma tattara sahihan bayanai kan ɓarnar da aka samu, domin gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace.
Ta bayyana cewa gwamnatin jihar na tausaya wa al’ummarta, kuma ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tallafa wa waɗanda iftila’in ya shafa.
Hajiya Binta ta ƙara da cewa hukumar za ta miƙa cikakken rahoton ziyarar ga gwamnatin jihar domin ɗaukar matakan gaggawa.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bin matakan kariya a lokacin damina, musamman wajen kauce wa wuraren da ke da haɗarin ambaliyar ruwa.
A nasu ɓangaren, wasu daga cikin waɗanda iftila’in ya shafa sun nuna godiyarsu ga gwamnatin jihar da hukumar SEMA bisa ziyartar su da kuma jajanta musu.
Sun roƙi gwamnatin jihar da ta ci gaba da tallafa musu, suna bayyana cewa da dama daga cikinsu sun yi asarar gidaje da sauran dukiyoyi sakamakon ambaliyar ruwa da iska.
