
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin mutane 28 ciki har da limamin Masallacin Izala na Ungushi, Imam Aliyu ne aka halaka a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka farmaki jama’a a ƙauyen Ungushi da ke Ƙaramar Hukumar Kebbe ta Jihar Sakkwato a daren Litinin.
Da yake tabbatar da labarin, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato, DSP Ahmed Rufa’i, ya ce yana da wuya a iya gano ainihin adadin waɗanda iftila’in ya shafa. Saidai, ya ce an gano gawarwaki guda 28 bayan aukuwar lamarin.
Mazauna sun ce maharan sun afka wa ƙauyen ne da dare, inda suka buɗe wa jama’a wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 22 waɗanda galibinsu fararen hula ne.
Kisan Imam Aliyu, wanda malami ne da ake girmamawa a yankin, ya girgiza mazauna, waɗanda suka ce cikin mamatan akwai manoma, ƙananan ‘yan kasuwa, jagororin addini da wasu ‘yan ƙauyen.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, harin ya haifar da fargaba acikin mazauna, saboda haka mutane da dama suka tsere daga gidajensu bayan samun labarin cewa ‘yan wasu ƙauyuka mafi kusa da su sun bar gidajensu domin neman mafaka a wasu yankuna.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ‘yan bindiga cikin adadi mai yawa suka shiga sassan Kebbe, inda suka farmaki jama’a da sace kayayyaki a shaguna da lalata wasu kadarori a ranar Juma’a.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar al’amarin a yankin amma ta ce tana kan tattara bayanai a kai.
Babban Hafsan Soji kuma Jami’i Kwamanda Janar GOC, na Sashe na 8 na Rundunar Sojin Nijeriya, Manjo-Janar Bemgba Koughna, ya ziyarci sansanin sojoji na Kebbe a ranar Litinin domin duba matakin tsaro da kuma tabbatar wa al’umma cewa dakarun tsaro a shirye suke su fuskanci barazanar tsaro a yankunansu. Haka kuma, ya gana da jagororin al’umma da mazauna wajen sauraren kokensu da kuma nazari kan halin tsaro a yankin nasu.
