Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A yayin da nake wannan rubutun iyalai da ’yan uwan jami’an ’yan sandan nan su 10 da ’yan ta’adda suka hallaka a yayin artabun da suka yi a yankin Makuku na ƙaramar Hukumar Sakaba a Jihar Kebbi, suna nan cikin alhini da jimami, sakamakon kisan gillar da aka yi musu.
Wannan babban koma baya ne ga harkar tsaro, da kuma yaƙin da ake yi da ’yan ta’adda da masu ɗauke da makamai suna cutar da al’umma. A yayin da ake kukan jami’an tsaro sun yi ƙaranci, ’yan ta’adda na samun goyon bayan matasa zauna-gari-banza don cimma manufofin su na son zuciya, suna kuma amfani da kuɗin fansa wajen sayen muggan makamai.
Sai dai a daidai wannan lokaci da ake cigaba da fuskantar ta’adi da ɓarnar da yaƙi da ta’addanci ke yi wa tattalin arziƙin ƙasar nan, da zamantakewar al’ummar ta, sai ga wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa tana yi wa ’yan Nijeriya, musamman jami’an tsaro na soja da iyalansu albishir da cewa, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ƙara musu albashi, tare da ba da umarnin ƙara ɗaukar matasa masu sha’awar ba da gudummawa a harkar tsaro, cikin aikin soja. Wannan babban abin a yaba ne ƙwarai da gaske, kuma ko ba komai za a ce gwamnati ta nuna da gaske take yi wajen warware matsalolin da suka dabaibaye harkar tsaro a ƙasar nan.
Sai dai kamar yadda muka sani ne, matsalar tsaro a Nijeriya ba ta tsaya ne kan ƙarancin jami’ai da ƙarin albashi kaɗai ba. Haka kuma matsala ce ta ƙwarin gwiwa, samar da shugabanci nagari a tsakanin jami’an tsaro na soji manya da ƙanana, samar da jin daɗin jami’an tsaro, da kuma yadda gwamnati ke ɗaukar batun tsaro da muhimmanci cikin manufofin ta da kasafin kuɗinta na shekara-shekara. Saboda haka, matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka a baya-bayan nan sun cancanci a duba su, ba kawai a matsayin matakan siyasa ba, amma a matsayin alamun cewa gwamnati ta fara fahimtar cewa rundunar da ta gaji ba za ta iya yin nasara a yaƙi da ta’addanci ba.
Muhimmi daga cikin manyan matakan gyare-gyare da gwamnati ta ɗauka ya haɗa da wannan al’amari na batun ƙarin albashi ga jami’an soja. Shekaru da dama, sojoji, ‘yan sanda, da sauran jami’an tsaro sun nuna haƙuri, juriya da jajircewa a yayin da suke sadaukar da rayuwarsu da ta iyalansu don fuskantar ƙalubalen tsaro da yanayin tashin hankali da ƙasar nan ke ciki, tada ƙayar baya, garkuwa da mutane, da rikicin ƙabilanci. Da yawa daga cikinsu sun yi aiki cikin wani yanayi mawuyaci, ana yaba musu a baki amma ba a ba su isasshen ladan da ya dace da gwagwarmayar su ta zahiri. A irin wannan yanayi, ƙarin albashi ba wai gyaran gudanarwa kawai ba ne. ƙoƙari ne na dawo da mutunci ga aikin da suke yi.
Wannan batu yana da muhimmanci sosai. Sojan da ke jin an manta da shi ba ɗaya yake da soja da ke jin ana ba shi kulawa da muhimmanci ba. Jami’in ɗan sandan da aka bai wa kayan aiki da kuma biyan haƙƙoƙin sa yadda ya kamata, ya fi iya yin aiki da kwarin gwiwa da ɗa’a fiye da wanda aka bari a fagen daga ba tare da kyakkyawar kulawa ba. ƙwarin gwiwa ba ya magance rashin tsaro shi kaɗai, amma yana shafar yadda hukumomi ke sauraron koke-koken jam’ian tsaro da ƙwararrun da suke ba su shawara. A yayin da jami’an tsaron mu ke aiki cikin ƙunci da takaici, abubuwan da suka daɗe suna rage wa jami’an mu karsashi, wannan mataki na inganta walwala, da jin daɗin ma’aikata ba alfarma ba ce; wajibi ne.
Haka kuma, gwamnatin ta ɗauki wasu matakai da ke nuna cewa ta fahimci matsalar tura jami’ai bakin daga. Janye ‘yan sanda daga aikin gadin manyan mutane, sannan da tura su wuraren da ake fuskantar matsalar tsaro, mataki ne mai kyau. Abin da gwamnati ta yi ya nuna cewa ba za a cigaba da ware wasu jami’an tsaro domin jin daɗin wasu ‘yan ƙalilan ba, alhali rayuwar yawancin al’umma na cikin haɗari. Aikin jami’an tsaro na farko shi ne kare rayuwar jama’a, ba don gata da samar da kariya ga wasu tsiraru ba. Wannan mataki na shugaban ƙasa, kodayake ba abu ne da muke fatan ya tsaya a takarda da fatar baki ba, abu ne da kowanne ɗan Nijeriya ke farinciki da shi, ba ma kawai ga sojoji da iyalansu ba. Saƙo ne mai muhimmanci da ke nuna cewa, gwamnati ta fara fifita muradun jama’a a kan jin daɗin masu mulki.
Kwanakin baya mun yi bayani kan alfanu da ƙalubalen da za a iya fuskanta da kafa rundunar ‘yan sanda na jihohi, amma duk da haka muna ganin matakin da gwamnati ta ɗauka a matsayin muhimmin abu. Tsawon shekaru, Nijeriya ta dogara ne da tsarin ‘yan sandan tarayya wanda yanayin gudanar da ayyukan su ke kawo jinkiri wajen kai ɗaukin gaggawa, sannan akwai tazara a tsakanin su da jama’a, sannan ba sa iya sauke nauyin da aka ɗora musu yadda ya kamata, saboda ƙarancin yawa da rashin wadatattun kayan aikin tsaro.
Ta hanyar ƙarfafa batun ‘yan sandan jihohi, ya nuna gwamnati ta amince da abin da mutane da dama suka daɗe suna cewa: matsalolin tsaro sun bambanta daga wuri zuwa wuri, don haka amsar su ma ya kamata ta kasance kusa da al’ummomin da abin ya shafa. Idan aka tsara shi da kyau, ‘yan sandan jihohi na iya taimakawa wajen inganta saurin ɗaukar mataki, tattara bayanan sirri, da kuma kula da al’umma yadda ya kamata.
Duk da haka, dole ne a yi taka tsantsan. ɗaukar matakai da nufin kawo gyara ba daidai yake da samun sakamako ba. Ba tun yanzu ba, ‘yan Nijeriya sun sha jin alƙawura da dama, kafa kwamitoci da yawa, da manyan jawabai kan tsaro, amma a ƙarshe abin da jama’a ke gani a zahiri bai taka kara ya karya ba. ƙarin albashi na iya ƙara wa ma’aikata musamman jami’an tsaro ƙwarin gwiwa, amma sai an aiwatar da shi cikin gaskiya kuma a kan lokaci. ɗaukar sabbin jami’an tsaro na iya kawo sauye-sauye a yaƙin da ake yi da ta’addanci, amma sai an horar da su da kyau kuma a sa ido a kansu. ’Yan sandan jihohi kuwa na iya inganta tsaro na cikin gida, amma sai an kafa tsauraran matakan kariya na doka da siyasa domin hana amfani da su wajen danniya da tauye haƙƙoƙin tsiraru da abokan adawa.
Irin tsare-tsaren da Gwamnatin Tinubu take ɗauka a ɓangaren tsaro da tattalin arziki abubuwa masu masu kyau sosai, musamman ga cigaban Nijeriya. A zahiri muna iya fahimtar yadda gwamnati ke magana da harshen da talakawa suke iya fahimta, duk kuwa da koke-koke da ake yi a wasu ɓatagarori, muna sa rai da fatan ganin an samu canje-canje masu tasiri ga rayuwar talaka. Gwamnati na ƙoƙarin nuna cewa ba za a canza fannin tsaro da karfi kaɗai ba; dole ne a canza shi cikin mutunci da girmamawa. Amma wannan girmamawa dole ne ta zama ta aikace. Ya kamata a gan ta a cikin albashi, kayan aiki, dabaru, gidaje, kula da lafiya, da kuma tallafin gaggawa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu wajen aikin tsaro.
