Dakarun tsaro sun ceto mutum tara bayan daƙile harin ‘yan bindiga a hanyar Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun Sashe ne 2 na Atisayen FANSAR YAMMA, sun yi nasarar daƙile wani harin ‘yan ta’adda na garkuwa da mutane da dama a Unguwar Rogo da ke Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda ta Jihar Zamfara, inda suka yi nasarar ceto wasu mutane guda tara, saidai maharan sun tsere da uku a yayin haka.

Rahotanni sun bayyana cewa, ana zargin maharan yaran jagoran ‘yan ta’adda mai suna Malam Shu’aibu ne, waɗanda suka ƙaddamar da harin da nufin ramuwa akan atisayen sojoji na kwanan nan kan dabar da masu taimaka mata ciki har da kama masu tsegumi guda bakwai da masu raba musu kayan amfanin yau da kullum da aka yi zargin suna yi wa jagoran ‘yan bindigar ne aiki.

Wani mazaunin yankin da ya nemi da sakaye sunansa, ya ce ana zargin waɗanda aka kama sun haɗa da masu taimaka wa aikin kai kuɗaɗen fansa ga ‘yan ta’adda ta hannun na’urar POS, yana mai cewa wannan shi ya sa suka shirya sace mutane da dama.

Wata majiyar tsaro ta ce, sojojin sun samu kiran gaggawa ne a lokacin da maharan suka afka wa yankin Unguwar Rogo, inda suka tare hanya da fara yunƙurin garkuwa da masu zirga-zirga. A cewarta, Shuaibu da makusantansa sun fusata ne kan kame masu taimaka musu yayin da suke yunƙurin siyan babura da fetur ga ‘yan bindigar.

Mazaunin ya ƙara da cewa, maharan sun yi amfani da damar fitar tsirrai a gonaki wajen yin kwanton-ɓauna akan masu zirga-zirgar. Ya ce, saboda haka ne jami’an tsaro suka shawarci manoma da ƙaurace wa shuka hatsin da ke yin tsiro mai tsayi, amma wasu sun yi buris da umarnin, don haka suka samar da maɓoya ga maharan.

Kazalika, ya ce an harbi mata guda biyu yayin harin waɗanda a yanzu suna halin karɓar magani. Saidai ba a samu ji daga bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ba, amma sojoji sun ce suna ƙoƙarin fitar da rahoto na musamman a kai.

By Babaji

Leave a Reply