Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙungiyar ‘yan jarida reshen kafofin yaɗa labarai (correspondent’s chapel) a Katsina Yusuf Ibrahim Jargaba ya yi kira ga ‘yan jarida da su nuna ƙwarewa da adalci wajen bada rahoto kan zaɓen 2027 da zai gudana a ƙasar.
Jargaba ya yi wannan kira ne a wani taron ƙarawa juna sani da ƙungiyar ta shirya wa ya’yan da wasu kafofin sadarwa a Katsina.
Ya bayyana cewa a Najeriya musamman Jihar Katsina ‘yan jarida na da rawar da zasu taka wajen abinda ya shafi zaɓe.Ya ƙara da cewa ta hanyar faɗakarwa al’umma za su fahimci yadda ake gudanar da zaɓe,za su san jam’iyun siyasar ƙasar da yan takarar su.
Akan haka ne Jargaba ya ce ya bayyana cewa ‘yan jarida na da muhimmanci wajen zama a tsakiya tsakanin masu zaɓe, ‘yan siyasa da sauran ma ruwa da tsaki.
A jawabin fatan alheri shugaban ‘yan jarida reshen Jihar Katsina Kwamred Aminu Dandago ya jawo hankalin manema labarai cewa suna da rawar da zasu taka wajen bada sashin labarai da zai baiwa al’umma su yanke hukuncin.
Kan zaɓen 2027, Dandagoro ya yi kira ga ɗaukacin ‘yan jarida da sauran ma su ruwa da tsaki da a haɗa kai wajen ingantaccen zaɓe da kowa zai aminta da shi.
A nasa jawabin, kwamishinan yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango wanda babban sakatare na ma’aikatar Alhaji Tukur Dan Ali ya wakilta ya jaddada ƙudirin gwamnatin Katsina na baiwa kowa damar gudanar da aikin sa a cikin kyakkyawar yanayi.
Ya kuma yaba wa ƙungiyar da ta shirya wani taron ƙarawa juna sani wanda yace zai taimakawa ya’yan ƙungiyar su ƙara fahimtar nauyin da ya rataya a wuyan su na bada sahihi labarai da zai gamsar da al’umma.
Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC da wasu malaman jami’ar Umaru Musa Yar’adua na sashin koyar da aikin jarida da na tarihi da tsaro suka gabatar da ƙasida a wajen taron.
