
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun Rundunar Sojin Nijeriya sun cimma gagarumar nasara akan harkokin ‘yan ta’adda, inda suka halaka mayaƙan ISWAP guda 21 a yayin wani hari, ciki har da manyan kwamandoji. Haka kuma, mayaƙa 26 da iyalansu sun miƙa wuya.
Daraktan Harkokin Yaɗa Labarai, Manjo-Janar Michael Onoja ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 21 ga Nuwamba, 2026, inda ya bayar da bayanan atisayen sojoji tsakanin 13 da 19 ga watan. A cewar sanarwar, hare-hare ta sama da dakarun suka ƙaddamar a tsakanin ranar Litinin da Talata a yankin Monguno da Arinna a kudancin yankin Tafkin Chadi da ke Jihar Borno sun kashe ‘yan ISWAP 21 yayin da wasu 10 suka samu munanan raunuka.
Ya ce, harin farko ya halaka mayaƙa bakwai, ciki har sa mambobin ƙungiyar da ke sashen ayyukan haɗa ababen fashewa (IED), da halaka wani ƙwararre a ciki. A cewarsa, hari na biyu a yankin Arinna ya yi ajalin mambobin kwamitin shura na ISWAP, wanda ya yi aiki a matsayin babban kwamanda, wato ƙa’idi na Sabon Tumbu da wasu mayaƙa guda 12.
Sannan, matsin sojoji ya tilasta wa ‘yan ta’adda 26 da iyalansu, da suka haɗa da mayaƙa takwas da mutane 18 ‘yan gidajensu, miƙa wuya ga dakarun tsaron a tsakanin 13 da 18 ga Nuwamba a yankunan ƙananan hukumomin Bama, Gwoza, Kukawa da Monguno na Jihar Borno. Waɗanda suka miƙa wuyan sune mata 12 da yara da suka tsere daga Buka Daloye a ranar 13 ga Nuwamba, da kuma wani ɗan ta’adda da ya ajiye makami tare da miƙa wuya a ranar 14 ga Nuwamba.
Cikin ababen da ɗan ta’addan ya miƙa akwai bindigar AK-47, akwatin harsasai guda biyar, alburusai 34 da ƙananan boma-bomai biyu. Kakakin sojojin ya bayyana cewa ‘yan ta’addar da suka miƙa wuya sun ce sun yi haka ne sakamakon matsin hare-haren sojoji da rikicin cikin gida tsakanin daba-dabarsu, wanda hakan ya sa suka fice daga cikin tafiyar.
Ya ƙara da cewa, sojojin sun kuma yi nasarar ceto ‘yan gudun hijira da suka tsere daga maɓoyar ‘yan ta’adda a yankin ƙauyen Zaha da ke kusa da tsaunukan Mandara a Ƙaramar Hukumar Gwoza, ranar Talata. Kazalika, ya ce sojoji sun kama masu taimaka wa ‘yan ta’adda da masu kai musu kayayyaki a jihohin Borno, Yobe da Kano, ciki har da mutanen da ake zargi da kai kayan yaƙi maɓoyar ‘yan ta’adda.
A Arewa maso Yammacin Nijeriya kuwa, Manjo-Janar Onoja ya ce dakarun Atisayen FANSAR YAMMA, sun yi nasarar ceto mutum uku da aka sace akan hanyar Anka zuwa Gada Mayya da ke Jihar Zamfara a ranar 12 ga Nuwamba, sannan sun kama wata motar ‘yan ta’adda.
A cewarsa, sojoji sun kuma halaka ɗan ta’adda guda yayin musayar wuta ƙauyen Aguba da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna a ranar 14 ga Nuwamba, inda suka ƙwato bindiga guda biyu da wayar hannu. Har ila yau, sojoji sun yi musayar wuta da ‘yan ta’adda a jihohin Filato da Kwara, wanda ya yi sanadiyyar ceto mutane da aka sace da ƙwato wasu makamai da dai sauransu.
