Sojoji sun ceto ɗalibai bayan daƙile yunƙurin garkuwa a shahararriyar makarantar Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’an Rundunar Sojin Nijeriya sun yi nasarar daƙile wani yunƙurin garkuwa daga ‘yan bindiga a wata fitacciyar makaranta mai suna Tafawa Ɓalewa College, Samaru a Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf da ke Jihar Kaduna. Al’amarin ya faru ne a ranar 18 ga Nuwamba, 2026, da misalin ƙarfe 11:55 na dare biyo bayan wani zargin zirga-zirgar ‘yan ta’adda a yankin farfajiyar makarantar.

A cewar majiyar soji da ta gana da ‘yan jarida, jami’an Sashe na 7 sun samu labarin zirga-zirgar wasu mutane da ake zargi ‘yan ta’adda ne a yankin, lamarin da ya sa suka hanzarta kai ɗauki. Ganin haka ya sa ‘yan bindigar suka janye daga ƙaddamar da atisayen.

Bayan haka ne dakarun suka gudanar da aikin bincike a farfajiyar makarantar da kewayenta amma ba su samu gamuwa da ‘yan bindigar ba. A lokacin ne suka ceto ɗalibai yayin da hukumomin gudanarwar kwalejin suka ƙirga ɗaliban don tabbatar da cikar adadinsu, inda bayan haka ne suka gano cewa ba a yi garkuwa da ko guda ba daga cikinsu.

A farkon Nuwamba ne dai sojoji suka ceto fararen hula 119 da ƙwato motoci takwas bayan gaba-da-gaba da ‘yan ta’adda da suka tare wata babbar hanya a Jihar Borno. Al’amarin ya auku ne a yankin Dutsen Kura zuwa Bulazarma zuwa Kamuya.

By Babaji

Leave a Reply