
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da ake saura ƙasa da mako guda a fara rajistar aikin Hajjin 2027, Ma’aikatar Aikin Hajji da Umara ta Saudiyya, ta amince da ƙara gurbin hajji guda 10,000 ga Nijeriya da kuma amince wa Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) duk da yin watsi da buƙatar haka da hukumar ta gabatar mata a karon fari.
A shekarar da ta gabata ne hukumomin Saudiyya suka rage adadin guraben hajjin da aka ba wa Nijeriya daga 95,000 da aka saba tsawon sama da shekara 20, zuwa 50,000 ga hajjin 2025 da 2026 kuma ake sa ran a yi haka a 2027. Rahotanni sun bayyana cewa, amincewar ta yanzu ta nuna cewa Nijeriya ta su ƙarin kujeru 10,000, wato zuwa 60,000 ga hajjin na 2027.
Bisa ga tsarin na kujeru 50,000 da aka ware wa Nijeriya ga na 2027, NAHCON ta raba su a tsakanin jihohi da ‘yan jigila masu zaman kansu, inda jihohi da jami’an tsaro suka samu 35,000, sauran 15,000 aka raba su ga masu aikin jigila.
Sakamakon cigaba da kira na a samar da ƙarin kujeru daga hukumomin jigilar alhazan jihohi da ‘yan jigila masu zaman kansu, NAHCON ta tunkari ma’aikatar Saudiyyan kan amsa buƙatar ga hajjin na 2027 bisa yawaitar masu neman zuwa hajji daga ƙasar.
Akan haka ne hukumomin Ƙasa Mai Tsarki suka amince wa Nijeriya ƙarin kujeru 10,000. A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’ar NAHCON Shafi’i Sani Mohammed ya fitar, ya ce an ware guda 7,500 ga hukumomin alhazan jihohi, sai kuma 2,500 ga kamfanonin jigila su bakwai.
