Ranar ’Yanci: Nijeriya ta hau sirdi, inji Tinubu

Spread the love

*Bai kamata ta koma baya ba, a cewarsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, Nijeriya ta samu sauyi mai muhimmanci a tafiyar tattalin arzikinta, yana mai cewa bayan shekaru uku na aiwatar da wasu gyare-gyare masu wahala tun hawan gwamnatinsa kan mulkin ƙasar, yanzu lokaci ya yi da za a mayar da hankali wajen tabbatar da wadata da inganta rayuwar ’yan Nijeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya gabatar wa ’yan Nijeriya a bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, inda ya ce gyare-gyaren da gwamnatinsa ta aiwatar sun kasance wajibi domin magance matsalolin tattalin arzikin da suka daɗe suna addabar ƙasar.

Shugaban ƙasar ya ce shekaru 66 da suka gabata Nijeriya ta fara tafiya a matsayin ƙasa mai ’yanci da ikon tafiyar da kanta, kuma tun daga lokacin ’yan Nijeriya suka ci gaba da kasancewa da fata cewa ƙasar za ta iya zama babbar ƙasa a Afirka mai haɗin kai, ƙarfi da wadata.

Ya ce tafiyar Nijeriya ba ta kasance mai sauƙi ba, domin ƙasar ta fuskanci yaƙi, mulkin soja, matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro da sauye-sauyen siyasa, amma duk da haka ’yan Nijeriya sun ci gaba da jajircewa wajen ganin ƙasar ta samu ci gaba.

Tinubu ya yaba wa manoma, ’yan kasuwa, malamai, matasa da jami’an tsaro, yana mai cewa irin ƙoƙarinsu da sadaukarwarsu ne suka taimaka wajen ci gaba da riƙe fata da burin samun kyakkyawar Nijeriya.

Ya ce ’yancin Nijeriya bai tsaya ga samun tuta, taken ƙasa ko zama cikin ƙasashen duniya ba, domin manufar ’yancin ita ce bai wa ’yan Nijeriya damar tsara makomarsu da gina ƙasar da za ta samar da dama, mutunci da ingantacciyar rayuwa ga jama’a.

Shugaban ƙasar ya amince cewa kafin shekarar 2023 tattalin arzikin ƙasar na fuskantar manyan matsaloli, inda talauci ke ƙaruwa tare da raguwar fata a tsakanin jama’a. Ya ce saboda haka gwamnatinsa ta yanke shawarar ɗaukar matakan gyara maimakon ci gaba da jinkirta matsalolin.

Tinubu ya kwatanta halin da Nijeriya ta shiga da mara lafiyar da aka gano yana da cutar daji, inda likita ya sanar da shi cewa maganin zai kasance mai wahala kuma mai raɗaɗi, amma zai iya ba shi damar samun sauƙi. Ya ce mutum na iya zaɓar shan magani domin ya yaƙi cutar ko kuma ya nemi maganin rage raɗaɗi kawai yayin da cutar ke ci gaba da yaɗuwa.

A cewarsa, tsawon lokaci an fi mayar da hankali wajen rage alamomin matsalar tattalin arziki maimakon magance tushenta, lamarin da ya sa aka ci gaba da kashe kuɗaɗe wajen tallafa wa wasu tsare-tsare da ba ma su ɗorewa ba ne.

Tinubu ya ce gwamnatinsa ta zaɓi ɗaukar matakan da suka dace domin gyara matsalolin tattalin arzikin ƙasar, duk da cewa matakan sun zo da wasu matsaloli da suka shafi rayuwar jama’a.

Ya jaddada cewa gyare-gyaren da aka yi ba su haifar da raunin tattalin arzikin ba, sai dai sun fuskanci matsalolin da suka daɗe suna wanzuwa.

Shugaban ƙasar ya ce bayan kimanin shekaru uku da fara gyare-gyaren, wasu alamomi na tattalin arziki suna nuna sauyi, ciki har da ci gaban tattalin arzikin ƙasar da ya ce ya haura kashi huɗu cikin ɗari a bana, tare da gudunmawar ɓangaren mai da wanda ba na mai ba.

Ya kuma ce satar ɗanyen mai ta ragu, hauhawar farashin kayayyaki ta sauko daga ƙololuwarta, an sake gina ajiyar kuɗaɗen waje, kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta samu daidaito, yayin da Nijeriya ta samu sama da dala biliyan shida daga fitar da kayayyakin da ba na mai ba a shekarar 2025, wanda ya ce shi ne mafi girma a tarihin ƙasar.

Tinubu ya ce waɗannan sauye-sauyen ba iƙirari ne kawai ba, yana mai cewa hukumomin duniya, masu sanya ido kan tattalin arziki da sauran masu ruwa da tsaki suna lura da sauye-sauyen da ke faruwa a ƙasar.

Ya ce bayan kammala matakin farko na gyaran tattalin arziki, Nijeriya ta kai wani sabon mataki inda babban abin da ya rage shi ne tabbatar da wadata mai yaɗuwa a tsakanin jama’a.

“Yanzu manufarmu mai sauƙi ce: wadata da za ta shafi kowa,” inji Tinubu.

Ya bayyana cewa wadata ba ta nufin ƙara girman tattalin arziki ko ƙara wasu alƙaluma kawai ba, sai dai samar da Nijeriya inda manomi zai iya noma cikin aminci, ya rage kuɗin noma, ya samu riba mai kyau, masana’antu su samu wutar lantarki mai inganci, ’yan kasuwa su samu damar samun rance, matasa su samu ayyukan yi, sannan abinci da sufuri su kasance cikin farashi mai sauƙin samu.

Shugaban ƙasar ya ce ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kai shi ne rage tsadar rayuwa ta hanyar rage kuɗin samar da kayayyaki da jigilar su zuwa kasuwanni.

Ya ce Nijeriya na da isasshiyar ƙasa da kuma jama’a da za su iya samar da abincin da ƙasar ke buƙata, don haka gwamnati za ta ƙara mayar da hankali wajen faɗaɗa noman rani da ban-ruwa, samar da iri da takin zamani, ƙara amfani da injinan noma, tare da zuba jari wajen ajiya da sufuri.

Ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da gina da kammala hanyoyi, layin dogo da tashoshin jiragen ruwa domin haɗa gonaki da masana’antu da kasuwanni.

A cewarsa, idan manomi ya rage kuɗin samar da amfanin gona, aka rage ɓarnar amfanin gona kafin ya isa kasuwa, masana’anta ta rage kuɗin wutar lantarki, motar dakon kaya ta isa inda za ta je cikin sauri, sannan yanayin kasuwanci ya ba ’yan kasuwa damar yin gogayya cikin adalci, hakan zai taimaka wajen rage farashin kayayyaki a kasuwa.

Tinubu ya ce wadata ba za ta samu ta hanyar rage farashin kayayyaki kaɗai ba, domin dole ne a samar da ayyukan yi masu amfani.

Ya ce kasancewar Nijeriya ƙasa ce mai yawan matasa na daga cikin manyan damar da take da su, saboda miliyoyin matasa ne ke shiga shekarun balaga a kowace shekara da baiwa, kuzari da buri.

Ya ce gwamnati na son mayar da wannan yawan matasa zuwa ƙarfin samar da kaya da ayyukan yi, maimakon ya zama sanadin rashin fata.

Saboda haka, ya ce samar da ayyukan yi, bunƙasa harkokin kasuwanci da masana’antu za su kasance cikin manyan manufofin gwamnatin tarayya.

Tinubu ya ce gwamnati za ta yi amfani da iskar gas wajen samar da makamashi ga sabbin masana’antu, ta tallafa wa masana’antun da ke ƙoƙarin farfaɗo da kamfanonin da suka daina aiki, ta faɗaɗa hanyoyin sadarwar zamani zuwa al’ummomin da suka daɗe ba su samu damar shiga tattalin arzikin zamani ba, tare da saka hannun jari wajen koyar da matasa ƙwarewar da kasuwanni ke buƙata.

Ya ce yana son ganin ƙarin ’yan Nijeriya suna samar da kayayyaki a cikin gida, gonakin Nijeriya suna ciyar da birane da samar wa masana’antu kayan aiki, sannan kamfanonin Nijeriya suna fitar da kayayyakin da suka samar zuwa sauran ƙasashen duniya.

Ya kuma bayyana burinsa na ganin matasan Nijeriya suna gina manyan kamfanonin fasaha da samar da ayyukan yi ga sauran matasa.

Sai dai Tinubu ya amince cewa har yanzu miliyoyin ’yan Nijeriya suna fuskantar matsaloli wajen samun abinci, biyan kuɗin makaranta, kuɗin magani da kuma kuɗin sufuri zuwa wuraren aikinsu.

Ya ce matsalolin da jama’a ke fuskanta ba su fara ne da gyare-gyaren shekaru uku da suka gabata ba, sai dai sakamakon matsalolin da suka taru tsawon shekaru, ciki har da ƙarancin samar da kayayyaki, rashin isassun abubuwan more rayuwa, ƙarancin damammaki da kuma raunin wasu hukumomin gwamnati.

Shugaban ƙasar ya ce ba za a iya kawar da dukkan matsalolin da suka taru cikin shekaru da dama cikin shekaru huɗu ba, amma gwamnati za ta iya sauya alƙiblar tattalin arzikin ƙasar tare da samar da damar da za ta fitar da mutane daga talauci a hankali.

Ya ce saboda haka gwamnatin tarayya na ƙarfafa shirye-shiryen tallafa wa gidaje mafi talauci, tare da inganta National Social Register domin tabbatar da cewa tallafin ya isa ga mutanen da suka fi buƙatarsa.

Ya kuma bayyana cewa Nigerian Education Loan Fund na taimaka wa ɗaliban da suka fito daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi wajen samun damar ci gaba da karatun manyan makarantu ba tare da matsalar kuɗin makaranta ta dakatar da burinsu ba.

Tinubu ya ce CREDICORP na bai wa ’yan Nijeriya masu aiki damar samun rancen sayen muhimman abubuwa kamar motoci, tsarin samar da hasken rana da na’urorin zamani, ba tare da sai sun tara kuɗi tsawon shekaru ba.

Ya ce gwamnatin tarayya, tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi, za ta ci gaba da ƙarfafa kiwon lafiya na matakin farko, ilimin bai ɗaya da sauran muhimman ayyukan gwamnati da talakawa suka fi dogaro da su.

Ya kuma ce tun daga shekarar 2023, gwamnati ta ci gaba da biyan albashi da fansho a kan lokaci, tare da yin gyare-gyare a tsarin fansho domin ƙara kare muradun ’yan fansho da sauran masu rauni.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa waɗannan shirye-shirye ba su kamata su zama madadin wadata ba, sai dai su kasance gada da za ta taimaka wa ’yan Nijeriya wajen kai wa ga samun ingantacciyar rayuwa.

“Manufarmu ba ita ce mu ƙara ƙwarewa wajen tafiyar da talauci ba. Za mu kayar da talauci,” inji Tinubu.

Ya ce kawar da talauci yana buƙatar lokaci, jajircewa da ci gaba da bunƙasar tattalin arziki tare da samar da miliyoyin damammaki masu amfani a faɗin ƙasar.

Tinubu ya ce a yanzu Nijeriya ta fara wannan sabon mataki ne daga wani yanayi mai ƙarfi, bayan gwamnati ta ɗauki wasu matakai masu wahala tare da aza tubalin da zai iya taimakawa wajen samun wadata mai ɗorewa.

Ya ce yanzu lokaci ya yi da ’yan Nijeriya za su gina makomar da za ta tabbatar da cewa yaran da za su zo nan gaba ba su fuskanci matsalolin da suka addabi ƙarnonin baya ba.

Shugaban ƙasar ya bayyana wannan sabon mataki da cewa “lokacin gyare-gyare ya yi aikinsa, yanzu kuma lokacin wadata ya fara.”

Ya ce burin gwamnati shi ne ganin alƙawarin da Nijeriya ta yi wa ’yan ƙasarta ya zama abin da ake gani a rayuwar yau da kullum, inda talaka, manomi, ma’aikaci, ɗan kasuwa, matashi da sauran jama’a za su samu damar cin moriyar ci gaban ƙasar.

A ƙarshe, Tinubu ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su ci gaba da kasancewa da imani da ƙasar, yana mai cewa Nijeriya ta gyara alkiblarta kuma bai kamata ƙasar ta koma baya ba.

Ya ce ƙasar na fuskantar wani sabon mataki na gina “ƙasar alkawari”, wato Nijeriya mai wadatar arziki da damarmaki, inda wadata za ta yaɗu ga jama’a, kowane yaro ya samu damar yin mafarki fiye da yanayin da aka haife shi a ciki, sannan ɗimbin albarkatun ƙasar su bayyana a rayuwar jama’a.

“Makomarmu tana gabanmu. Tubalinmu yana da ƙarfi. Alƙiblamu a bayyane take. Don haka mu ci gaba. Kada mu waiwaya baya,” inji Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya taya ’yan Nijeriya murnar cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, tare da addu’ar Allah ya albarkaci ’yan Nijeriya da Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply