Dakta Steven ya gargaɗi matasa kan tayar da zaune tsaye

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Babban sakatare a ma’aikatar matasa da raya wasanni ta jihar Nasarawa Dakta Stephen Iliya Sasetu ya yi kira na musamman da a riƙa shigar da matasa cikin ayyuka masu amfani domin daƙile zaman banza da kuma inganta zaman lafiya a jihar.

Sasetu ya bayyana haka ne ranar Talata na mako da ake ciki yayin da yake jawabi ga manema labarai a ofishinsa dake ma’aikatar a Lafia gabanin gudanar da ayyukan bikin ranar matasa ta duniya na bana.

Yace akwai buƙatar a haɗa kan matasa tare waje guda a kuma yi musu jawabi don a saurari matsalolinsu da kuma wayar da su kan bangarori masu kyau da marasa kyau na rayuwa.

A cewarsa irin wannan mu’amala za ta bai wa ma’aikatar damar samun gudummawar ra’ayoyinsu bisa ga ayyukan da ke ƙarƙashin ta.

Babban sakataren ya kuma bayyana cewa ayyukan da aka tsara don bikin sun haɗa da tattakin lafiya da kuma tattaunawa ta yanar gizo da za su mayar da hankali kan taken bikin na bana musamman kan batun lafiyar hankali.

Yace lafiyar hankali tana da matuƙar muhimmanci domin tana shafar lafiyar jiki da dangantaka da kuma yadda mutum ke hulɗa da al’umma musamman a lokacin da jihar ke shirin shiga zaɓe.

Dakta Steven Iliya Sasetu yace ma’aikatar ta yi rijistar ƙungiyoyin matasa daban-daban a faɗin jihar domin inganta zaman lafiya a yankunansu yana mai ƙarfafa wa matasa gwiwa da su nisanci tashin hankali.

A kan batun rashin aikin yi da zaman banza babban sakataren ya ce gwamnatin jihar na ɗaukar matakai don magance matsalar. Ya bayar da misali da ƙaddamar da shirin Sule Economic Empowerment Development Scheme wato SEEDS, a turance da gwamna Abdullahi Sule ya yi kwanakin baya wanda kimanin matasa 50 ne aka bai wa tallafi.

Ya bayyana cewa idan an shigar da matasa cikin ayyuka masu amfani zai rage yiwuwar amfani da su wajen tarwatsa ayyukan zaɓe yana mai cewa dole ne a juya ƙarfinsu zuwa harkoki masu amfani.

“Mun san cewa da zarar an shigar da matasa cikin ayyuka masu amfani matsalar za ta ragu. Su ne mutanen da ke da ƙarfi mai yawa. Idan ba a amfani da su yadda ya kamata, ba za a karkatar da su wajen aikata mummunan abu,” in ji shi.

Daga ƙarshe Sasetu ya buƙaci matasan jihar da su kuma rika amfani da damammakin da gwamnati ke samarwa yana mai tabbatar musu cewa ƙofar ma’aikatar a buɗe take a ko yaushe ga ra’ayoyi da shawarwarin da za su taimaka wajen cigaban jihar musamman daga gare su.

By ukarofi

Leave a Reply