Mutane biyar sun mutu sakamakon rushewar gine-gine a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Mutane biyar ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 10 suka tsira bayan rushewar wasu gine-gine guda biyu da suka faru a ƙananan hukumomin Kumbotso da Fagge na Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar a unguwar Gaida da ke Kumbotso, da kuma Kurna da ke Fagge. Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ce ta samu kiran neman agaji da misalin ƙarfe 2:34 na rana da kuma 2:40 na rana, bi da bi.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Abdullahi, ya fitar ranar Lahadi, ya ce ginin da ya rushe a Gaida, kusa da gidan mai na Salbas, gini ne da ake kan ginawa mai girman kusan ƙafa 50 da 50, wanda ya rufta kan ma’aikata shida.

Ya ce jami’an kashe gobara daga hedikwatar hukumar sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka ceto ma’aikata biyu da ransu, su ne Muhammad Hassan, mai shekara 17, da Khalid Abubakar, mai shekara 19.

Sanarwar ta ce an kuma ceto wasu ma’aikata huɗu a sume, amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsu. Mutanen su ne Sunusi Surajo, mai shekara 18; Bashir Ibrahim, mai shekara 20; Ibrahim Ibrahim, mai shekara 25; da Abubakar, mai shekara 30.

An kwashe dukkan ma’aikatan shida zuwa asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad, daga nan kuma aka miƙa su ga ɗan sanda mai suna Inspector Adamu Garba na ofishin ƴan sanda na Kofar Wambai.

A wani lamari na daban, ginin makarantar Islamiyya mai suna Khadija Idris Bala, da ke bayan makarantar firamare a Kurna, ƙaramar hukumar Fagge, shi ma ya rushe.
Hukumar kashe gobarar ta ce jami’anta daga ofishin kashe gobara ta Kurna sun ceto ɗalibai takwas daga cikin tara da lamarin ya rutsa da su, waɗanda shekarunsu ke tsakanin 12 zuwa 15.

Sai dai ɗaliba ta tara, Khadija Muhammad, mai shekara 14, an ceto ta a sume, amma daga baya aka tabbatar da mutuwarta.

Kazalika, sanarwar ta ce daga bisani an miƙa ɗaliban da abin ya rutsa da su ga shugaban makarantar, Muhammad Gambo Usman.

Hukumar ta ce a halin yanzu ana gudanar da bincike domin gano musabbabin rushewar gine-ginen guda biyu.

Da take ƙarin bayani kan abubuwan da suka faru, hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta buƙaci masu gine-gine, ƴan kwangila da ma’aikatan gini su kiyaye matakan tsaro tare da bin ƙa’idojin da hukumomi suka amince da su, musamman a lokacin damina.

Hukumar ta kuma yi kira ga jama’a da su riƙa ba da rahoton duk wani lamari da ya shafi rushewar gini cikin gaggawa, domin bai wa jami’an ceto damar isa wurin cikin lokaci tare da rage asarar rayuka.

Rushewar gini a Kwanar Yashi, wannan sabon lamari da ya zo kwanaki kaɗan bayan da hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ceto mutane 16 daga baraguzan wani ginin da ya rushe a yankin Dan Dinshe, Kwanar Yashi, ƙaramar hukumar Fagge. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Asabar, 8 ga Agusta, 2026, bayan wani ginin mazauni mai girman kusan ƙafa 20 da 30 ya rushe ba zato.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce hukumar ta samu kiran neman agaji da misalin ƙarfe 4:32 na asuba. Ya ce bayan samun kiran, jami’an hukumar daga hedikwata sun garzaya wurin, inda suka tarar da ginin mazaunin ya rushe.

Abdullahi ya ce jami’an ceto sun fitar da mutane 16 daga cikin baraguzan ginin, ciki har da yara uku da aka gano a sume.

Yaran su ne Affan Yusuf, mai shekara biyar; Hassana Yusuf, mai shekara bakwai; da Ummulkursum Yusuf, jaririya mai wata tara. Ya ce ayyukan ceto sun ci gaba domin gano wasu mutanen da ake zargin har yanzu suna ƙarƙashin baraguzan ginin.

Hukumar ta ce har yanzu ba a gano musabbabin rushewar ginin ba, yayin da aka fara gudanar da bincike kan lamarin.Ta kuma buƙaci jama’a da su ɗauki matakan kariya, musamman a lokacin damina, domin kauce wa sake faruwar irin waɗannan hadurran.

Wannan sabon lamari ya faru ne ƙasa da wata guda bayan rushewar wani gini mai hawa uku da ake kan ginawa a ƙaramar hukumar Nasarawa ta Jihar Kano, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu uku.

By ukarofi

Leave a Reply