Kwamred Maiwada ya zama shugaban NLC na riƙo a Katsina

Spread the love

ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Katsina, ta naɗa Kwamared Nasiru Wada Mai’adua a matsayin zhugaban ƙungiyar na riƙon ƙwarya.

Naɗa shi shugaban ƙungiyar na riƙon ƙwarya ya biyo bayan, aje muƙamin da shugaban ƙungiyar na Jiha Comrade Hussaini Hamisu Yanduna ya yi bayan zama babban Sakatare a Gwamnatin Jihar Katsina.

Kwamred Nasiru Wada Mai’adua kafin naɗa shi muƙamin shugaban ƙungiyar ƙwadagon na riƙon ƙwarya, shine shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ( NULGE )ta Jihar Katsina.

By ukarofi

Leave a Reply