
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta zaɓi wasu rumfunan zaɓe guda 17,656 a sassan jihohi 36 na faɗin Nijeriya har da Abuja, domin tantancewar gwaji da ɗora sakamako, wanda za a yi a ranar Asabar, 28 ga Nuwamba a matsayin ɓangare na shirye-shiryen zaɓukan 2027.
Za a gudanar da aikin ne daga ƙarfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na rana, wanda aka shirya da nufin gwada aikin na’urar tantance masu zaɓe ta Bimodal Voter Accreditation System (BVAS), gwada hanyoyin tantancewa da gano ƙalubalen da ka iya bijirowa da magance su gabanin zaɓukan 2027. INEC ta sanar da haka ne ta sahihin shafinta na X, inda ta ce za a gudanar aikin ne a rumfunan zaɓe biyu daga kowane yankunan rajista guda 8,838 na faɗin ƙasar.
Wani bayani na jaddawalin da hukumar ta fitar ya nuna cewa jimillar rumfunan zaɓe 17,656 ne aka zaɓa, wato an samu ragin 20 daga 17,676 da ake tsammanin bisa ga sanarwar zaɓin rumfa biyu a kowane yankin rajista.
Bayanin rumfunan zaɓen a sassan jihohin ya nuna cewa Kano ce take da mafi yawa na guda 968, sai Katsina mai 718 and Oyo da ke da 702. Osun tana da 664 Akwa Ibom 658, Anambra 652 da Ribas mai 638, sai Borno mai 622 da kuma Imo mai guda 610. A wani ɓangare, Abuja tana da mafi ƙarancin rumfuna na 124, sai Bayelsa 210 da Gombe mai 228.
Bayanin hakan a matakin shiyya ya nuna cewa Arewa maso Yamma ce take da mafi yawa, wato 4,002, wanda ke wakiltar kaso 22.7 na jimillar baki ɗaya adadin. Kudu maso yamma na da 3,088 a matsayi na biyu, wato kaso 17.5, yayin da Kudu maso Kudu ke da 2,874 ko kaso 16.3. Arewa ta Tsakiya tana da rumfa 2,785 mai wakiltar kaso 15.8, sai Kudu maso Gabas mai 2,489, wato kaso 14.1 da Arewa maso Gabas mai 2,418 (kaso 13.7).
Kazalika, INEC ta wallafa jaddawalin zaɓaɓɓun rumfunan domin wayar da kan jama’a, samar da bayanan jihohinsu, ƙananan hukumomi, gudumomi, sunayen rumfunan zaɓe da lambobi da za a yi amfani da su wajen gane su.
