Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kira na neman a cire Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, mai shekara 92, ya ƙara ƙarfi bayan wata baƙuwar yawon buɗe ido daga ƙasashen waje ta zarge shi da cin zarafinta a lokacin ziyarar da ta kai fadar sa a ranar 14 ga Nuwamba.
Bazawara, wadda ta bayyana kanta da suna Mirka a Instagram da @beduinqa, ta ce tana kan yawon buɗe ido na kwanaki 30 a Najeriya, a matsayin ƙasa ta 184 a cikin tafiyar da ta shirya na ziyartar ƙasashe da yankuna 197 na duniya. Ta ce an kai ta wani ɗaki mai kyau a fadar, inda ta zauna da Sarkin suka yi magana.
Ta yi zargi cewa Sarkin ya fara riƙe hannunta yana wasa da shi, sannan ya rungume ta, ya sumbace ta a kumatu, kafin ya taɓa ƙirjinta ba tare da amincewarta ba. Ta ce ta yi masa ihu tana cewa “Sarki, a’a, a’a, a’a, ba za ka iya taɓawa ba,” amma ya yi dariya kawai.
Ta ce abin ya ba ta mamaki musamman saboda ta zagaya sassa daban-daban na Najeriya ba tare da ta fuskanci cin zarafi a wuraren jama’a ba, amma abin ya faru a cikin fada inda ake sa ran mutunci da daraja. Ta ce ta ɗauki bidiyon ne da tabarau na Meta, kuma ta jira har ta bar Najeriya kafin ta wallafa shi.
Wanda ya fi fitowa fili a cikin masu kira shi ne fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi. Ya rubuta a Facebook cewa: “Duk wani Sarki da aka samu da laifin ɗabi’ar rashin mutunci, a cire shi a maye gurbinsa nan take domin kare mutunci, daraja da sahihancin cibiyar sarauta.”
Gumi bai ambaci Sarkin Daura da suna ba, kuma bai ce yana da laifi ba. Matsayinsa sharadi ne, cewa idan aka tabbatar da laifi, to a cire Sarkin.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam na Amnesty International Nigeria ma ta yi kira ga Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗabda rundunar ’yan sandan Najeriya da su gudanar da bincike mai gaskiya da zaman kansa kan zargin, tare da tabbatar da adalci idan aka tabbatar da laifin, ba tare da hukuncin kisa ba.
Sauran masu kira sun haɗa da lauya Pelumi Olajengbesi da CITAD, waɗanda suka nemi a gudanar da cikakken bincike, da kuma mai fafutuka a kafafen sada zumunta, VeryDarkMan, da sauran masu sharhi a yanar gizo da ke neman a cire Sarkin.
A ɓangare guda, Majalisar Masarautar Daura, ta bakin mai magana da yawunta, Ibrahim Daura, Sarkin Labaran Daura, Alhaji Ibrahim Usman Murtala ya tabbatar da cewa Masarautar na nazarin bidiyon don tabbatar da sahihancinsa da kuma ko an gyara shi ko an ƙirƙira shi da fasahar zamani. Yace ce za ta fitar da sanarwa a hukumance bayan ta kammala nazarin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, Sarkin bai fitar da martani na kansa ba, Majalisar Masarauta da Gwamnatin Jihar Katsina ba su fitar da sanarwa a hukumance ba, kuma ba a sanar da sakamakon wani bincike na ’yan sanda ba.
