Ma’aikatar Tsaro ta goge wallafar tallata taron APC yayin cece-kucen al’umma

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ma’aikatar Tsaro Tarayya ta goge wata wallafa daga sahihin shafinta na dandalin X da ke tallata gangamin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu karo na biyu a Ibadan, Jihar Oyo, bayan shan suka akan amfani da dandalin gwamnati wajen tallata harkokin jam’iyya daga ɓangaren al’ummar ƙasa.

Wallafar ta sanar da cewa za a yi taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC wanda aka gudanar a ranar Asabar, 21 ga Nuwamba, kuma ta ruwaito cewa Ministan Ma’aikatar, Christopher Musa (janar mai ritaya) ya kai ziyarar dubiya a wajen taron bayan jami’an tsaro sun yi bincike a ka a daren da ya gabata kafin taron.

A cikin wallafar an ga wasu hotunan da suka ƙunshi ziyarar ministan. Saidai ma’aikatar ba ta bayyana dalilin da ya sa ta cire wallafar ba. Ta ƙunshi cewa Shugaba Tinubu da wasu manyan jami’an jam’iyyar ne za su halarci taron.

Wannan al’amari dai ya tayar da hazo acikin al’umma musamman ganin yadda hakan ya shafi ingancin ayyukan cibiyoyin gwamnati da rashin ware kai daga ɗaukar ɓangare a harkokin siyasa, inda wasu ke ganin hakan a matsayin saɓa wa ƙa’idar aiki daga hukumomin gudanarwar ma’aikatar.

Hakan na zuwa ne ƙasa da wata biyu da za a gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun dokokin ƙasa a Junairun 2027 da ke ƙaratowa yayin da jam’iyyun siyasa ke cigaba da ɗaura ɗamarar gwabzawa a tsakaninsu.

By Babaji

Leave a Reply