NFF ta sallami tawagar jagorancin Super Falcons ta Koci Madugu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kwamitin Zartarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF), ya tsige tawagar gudanar da harkokin ‘yan wasan Super Falcons ƙarƙashin jagorancin Justine Madugu, hukuncin da ya fara aiki a nan take.

NFF ta sanar da haka ne a wata sanarwa da ta wallafa a sahihin shafinta na X a ranar Litinin.

Super Falcons ta shiga mawuyacin hali yayin buga wasannin gasar Kofin Ƙasashen Afirka na Mata WAFCON, wanda aka gudanar a ƙasar Moroko.

Nijeriya ta shiga gasar ne a matsayin wadda take riƙe da kofin kuma ta lashe har sau goma a tarihinta. Saidai an yi waje da ita ne a wasan dab da na kusa da na ƙarshe a wasan da ta kara da Kamaru, wanda aka tashi 1 da 0.

Bayan ‘yan kwanaki ne tawagar ta sake yin rashin nasara da ci 2 da 1 a hannun Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu, lamarin da ya kawo ƙarshen fatanta na samun gurbi a Gasar Kofin Duniya na 2027 da ke tafe. Wannan al’amari ya sa ba za ta shiga gasar ba a karon farko tun bayan farawa a 1991.

By Babaji