
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori ya gabatar da wasiƙar godiya ga Hajiya Hajara Abdullahi ta Diso Quarters da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a jihar, yayin yaba wa ƙoƙarinta na taimaka wa al’umma musamman kan gyara ofishin ‘yan sanda na Shiyyar Gwale da ta gudanar.
Ya ce, wannan hoɓɓasa da Hajiya Hajara ta yi na wakiltar gagarumar gudumawa ga harkar tsaro a yankin. A cewarsa, tana bayar da tallafi ga ayyukan shiyyoyin ‘yan sanda a sassan jihar da nufin inganta wuraren ayyukan jami’ai da bunƙasa lamuran hidimta wa al’umma.
Da yake damƙa mata wasiƙar a Hedikwatar Rundunar, CP Bakori ya bayyana hajiyar a matsayin ɗaya cikin dubu kuma abokiyar hulɗa a lamuran ‘yan sanda ta gaske.
Ya sanar da cewa, ƙoƙarinta wajen bayar da kariya da walwalar yankinta na nuna ƙwarin-gwiwa da biyayya ga sauke nauyin ɗaiɗaikun al’umma, yana mai addu’ar Allah ya ƙara mata arziƙi mai albarka da kuma saka mata da kyakkyawan sakamako.
A nata jawabin, Mai taimaka wa Gwamnan Kano ta musamman kan harkokin ‘yan sanda, Hon. Hajiya Maimuna Umar Sheriff, ta yaba wa Hajiya Hajara bisa abin da ta kira da “abin koyi”, inda ta ce ta haka ne ‘yan ƙasa za su riƙa tallafa wa ƙoƙarin gwamnati wajen ceto yankuna.
Ta kuma jaddada aniyar gwamnatin jihar, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ƙoƙarin tabbatar da walwala da tsaron dukkan mazauna, tana mai kira ga sauran ɗaiɗaikun al’umma da ƙungiyoyi da su yi koyi da ita, kamar yadda kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, 17 ga Agusta, 2026.






