Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Bikin Ranar Hausa ba shi da asali ko kaɗan kuma waɗanda ke kanbama yin sa ba Hausawa ba ne. Mutane masu sa ka hula hana sallah wai su ne za su yi taron raya al’adun Hausawa!
Wannan biki da wasu matasa su ka kirkira ba tare da tuntuɓar dattawa da sauran manyan malaman jami’a ba musamman ABU, BUK da UDUS na nuna yadda tarbiyya ta taɓarɓare a tsakanin matasa da ke yin abun da su ka ga dama don sun ga yadda Dan Daudu ma zai yi ta yin shakiyancinsa amma ba a damu ba, in ma mutum ya yi magana a zarge shi da tsaurin ra’ayi ko a ce wai “ai raha ce Malam, kai ba ka san raha ba?”
Hausa na cikin manyan harsunan duniya 11 kuma ba wani babban harshe da ma’abotansa ko masanansa da su ka ware rana wai don bukinsa. Hatta Hausa ma da wasu ke rawar jiki don c!mma wani burinsu na ƙashin kai, ba wanda ya ba da hurumin yin wannan biki. Haƙiƙa wannan abu da ya ɓullo ‘yan watanni kalilan da su ka wuce kaskantar da Hausa ne da cin zarafin al’ummar Arewa da sauran kasashe da ke amfani da harshen a lamuransu na rayuwa.
Ai kullum ranar Hausa ne kuma kullum harshen Hausa bunƙasa ya ke yi kazalika sana’o’i kuma wai da za a farfaɗo da su, a farfaɗe su ke don da alamu ba wani mutum daya tak a cikin masu karambanin nan da ya iya ko sana’a ɗaya ta Hausawa, don haka ba su san ma mebne ne al’adu ko sana’o’in Hausa ba. Hasalima mutanen da ke wurgo turanci in su na Hausa ko ke c√sa kokon kansu a cikin hula hana-sallah wai su ne za su raya al’adu? Kai wadannan sun ba rna Hausawa ba nekuma ya kamata a taka mu su birki tun kafin su ɓullo da wasu m!yagun dabi’u su ce na Hausawa ne ta hanyar tallata su a kafofin bulus na Bello-Badum wato soshiyal midiya da ko a rumfar sayar da barasa za su kunna waya su cilla shirme su ɗauka wata gwaninta su ka yi.
Tun bara na ga wasu na muhawara kan ranar a tsakanin masu cewa 27 ga Yuli ne wasu na cewa a 26 ga Agusta ne. Wa ya ba su izinin sanya rana da sunan harshen Hausa? In fa za a saka rana a madadin harshen Hausa ya zama wajibi aƙalla a Arewa maso yamma a riƙa ayyana ranar a matsayin hutu da kuma yin jawabai da iya harshen Hausa kaɗai a ranar a lamuran gwamnati da su ka shafi jama’a. To amma don rashin amfanin yin hakan shi ya sa ba zai yiwu ba. Don wasu ‘yan matasa sun je Daura ko wani gari da nuna su na kishin Hausa ba shi ne lasisin da za su bugi kirji su ayyana rana musamman wai ta Hausa ba. Kai waɗannan sun samu rana don haka su ke shanya. Zan yi mamaki a ga wani dattijo ko masanin harshen Hausa ya hararci taro har ya yi jawabi da sunan ranar harshen Hausa ta shekara.
Tun farkon wannan wuce gona da irin, na yi magana da nuna taron ba daidai ba ne don wulaƙanci ne ga Hausa da Hausawa sai wani Bazalle ya yi wuf ya ce ai Larabawa ma na yin taron ranarsu! Nan na yi ma sa gyara da cewa ba taron harshen Larabci su ke yi ba, taro ne na ƙasashen Larabawa DUWAL al-KHALEEJ/GULF STATES don harkar diflomasiyya ba bunƙasa Larabci ba, don tun da Allah SWT ya saukar da Alƙur’ani da Larabci, harshen ya gama bunƙasa ila yaumil kiyamati.
Za a nuna rawar gargajiya a taron Zallawa wai na ranar Hausa don kyakkyawar al’ada!
Shin tikar tikar rawar banjo kyakkyawar al’ada ce?
Wallahi duk yadda ka zayyana Zallawa da nuna kutungiilar zagon ƙasa ga Hausawa da al’ummar Arewa ba za ka yi wani wuce gona da iri ba. In ba ‘yan arafta ba, ta yaya nuna rawar gargajiya zai zama kyakkyawar al’ada ba shagalin ‘yan ta-more ba?. A nan ya dace ma mu duba shin ranar Hausa ce inda a ke tsammanin tattaunawa kan yadda za a ceto harshen daga Zallallu masu wurgo Turanci a na tsakiyar Hausa ko ranar al’ummar Hausawa ce da za a ga mutane masu kamala da suturar gargajiya ba wurga kokon kai a hular hana-sallah ba, da ‘yan karyar Hausa Zalla ‘yan barandar AIFOB ke yi ba ko kunya?
Tabbas duk mai hankali da nazari a duniya idan ya ji za a yi rana ta Hausa kamar tarukan da a ke yi a makarantun boko, tunaninsa zai tafi kan ilimin ADABI ne wa in ma na BAKA/gargajiya ko na ZUBE/zamani da hakan ya kunshi tatsuniyoyi na jan hankalin yara su zama gwaraza da riƙon amana da kuma tarihi mai kyau. A nan kawai sai mu ka ga wasu na nuna za su baje kolin RAWAR GARGAJIYA! To ai wannan kawai taron Dan Asharalle ne LALE WARE GAJA a yi rawa a yi juyi shikenan dama an daina batun rawar banjo ga wasu ‘yan kwangila za su farfaɗo da rawar.
Kafin ma mu leka nunin sana’o’i da ya yi hannun riga daga masu sana’ar rufe kansu ruff a salula su na yayata izgilanci, mu kammala wannan batu na nuna rawa. Shin dama ‘yan dandi gidan su ‘yar gagara ba sa rawa ne? shin an daina tikar rawa ne shi ya sa Zallawa ke neman farfaɗo da rawa? ai kowa ya san yunkurin da a ke yi na ceto al’ummarmu daga lalacewa ta hanyar tikar rawa da fasikanci zuwa tafiya tsangayar karatun Alƙur’ani da ma shiga makarantun boko don samun ilimin zamani. Don haka wadannan m!yagun mutane in ba a taka mu su birki ba, to wasu za su iya dauka tikar rawar banjo kyakkyawar al’ada ce ta Hausawa, tir.
Ya zama wajibi Hausawa su fito su takawa mutanen nan birki don rainin ya kai kan iyaka saura kadan tura ta kai bango ta tsokanar Musulmi da Musulunci. Mutanen nan na kwangilar ture duk wani garambawul da Musulunci ya yi wa al’ummar Arewa ne zuwa sakarci da hawa borin iskar na-uwale wani ya yi tsalle can sama ya dirko kan duwawunsa timmm bakinsa na kumfa.
Sam sam rawar banjo ba kyakkyawar al’adar Hausawa ba ce amma ɗabi’ar waɗannan mutanen ne mazauna gefen garuruwan Hausawa masu la’asariyya a gidan barasa. Wallahi ba za su iya wannan makirci ba kuma ko za su yi ruwan maliyan bakaken maganganu da zunduma ashar karyarsu ta sha karya. Mu je zuwa mahaukaci ya hau kura.
Taron Zallawa wai ranar Hausa zai nuna sana’o’in Hausawa kamar kira, jima da saka. Duk Zallawa ba su da takamammiyae sana’a gabanin kwangilar zallanci.
Akwai ruɗu mai yawan gaske ga yadda wasu Zallawa ba izinin cibiyoyin Hausawa balle wata jami’a zuwa majalisar ɗinkin duniya su ka ƙirƙiri ranar Hausa. Mutanen nan sun ce za su baje kolin sana’o’in Hausawa kamar kira da jima! Shin me ya hada sana’a da AZANCIN HARSHE ko AL’ADA? Sana’a hanya ce ta dogaro da kai kuma sam ba ta shafi harshe ba. Idan a na batun ranar al’ummar Hausawa ne za a iya kawo sana’a da yanayin dabi’ar al’ummar.
Ni dai ban ga ko daya daga Zallawan nan na wata sana’a ba fiye da ruruta wannan fitina da ke zama barandancin neman kafa Biyafara da Midil Bel. Shi babbansu ma ɗan lakada-kawas wai a 2014 ya gama makaranta, nan nan jajiberin shekarar da marigayi shugaba Buhari ya hau mulki. Haƙiƙa har dai mutane ba su da sana’a za su iya yin caraf su karbi tayin dillancin dafin maciji don zubawa a kogin ƙauyensu don a rage yawan jama’a. To wanda sana’arsa hawa wayar salula ya yi ta shirga karya da murde wuyan tarihi, wace sana’a zai nunawa jama’a? in makeri ne ya zauna a maƙerar anguwarsu ma na.
Ba ya ga amfani da manhajar AI don yayata hotunan tafiye-tafiye ko zuwa wajaje na karya miraran, daya daga mafi zallewa ya nuna kansa ya na zagin wasu karnuka biyu waɗanda ba mamaki sana’rsa kenan k!won karnika da ta yiwu sana’ar da zai kai talla kenan wajen taron don dama ba shi da wata alaka ta kirki da Hausa kuma gidansu ma mabiya Yammawa ne. Nan ne ma ya kushe mataimakin shugaban ƙasa dungurungum ya buƙaci lallai a sauya shi a takara a mika ta ga jami’in soja da bai fito siyasa ba Janar Christopher Musa. Tun da shugaba Tinubu ya sake ayyana sunan Kashim sai Bazallen ya yi gum ya san farafagandarsa ta ts!ya ta daki dutse ta tarwatse kamar Terwase Akwaza na Binuwe.
KAMMALAWA
Taron da za a yi tsammanin ADABIN HAUSA a ji salon harshe sai kuma wai za a nuna yadda a ke kira da jima? Ba mamaki tun da mashirya taron ma ai ba Hausar su ka iya ba balle mu ji SHAHO YA SHARE SHEHU DA MARI YA SHEKA SAMA ko AUDU MA’AUNIN AUDUGA YA AUNA AWUN AUDUGAR MADUGU BUHU HUɗU ko cire soke a jikin danga hatta jama’a watsin… ha ha masu wurgo Turanci a tsakiyar Hausa ba sa iya ko ambata sunan NIJERIYA da muryar Hausawa sai ƙaƙalen Gwarawa NIJEIRIYYA ai sa fake da abubuwan da ba su da alaƙa da iƙirarin da su ka ambata wai ranar Hausa! To in ba tsoro ba ya zama tikitin shiga tsakiyar taro kowannensu ya nuna sakamakon jarrabawarsa ta Hausa a firamare ko sakandare, maki nawa ya samu. CI DA BUGUZUM.
