21
Apr
Daga JABIRU HASSAN Duk da irin ƙoƙarin da gwamnonin arewacin ƙasar nan ke yi, akwai buƙatar su ƙara himma wajen ɓullo da shirye-shirye waɗanda za su bunƙasa yankin ta fannoni daban-daban. Yanzu lokaci ya yi da gwamnoninmu za su zamo masu ƙoƙarin kafa managarcin ginshiƙin farfaɗo da yankunansu bisa la'akari da buƙatun kowane ɓangare kamar yadda muke gani a ƙasashen da suka ci gaba. A yankinmu na arewacin ƙasar nan, akwai mabambantan buƙatu da ke kowane sashe da kuma kowane ɓangare waɗanda idan aka sami nasarar aiwatar da su za a kasance cikin yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali. Akwai abubuwa da…