Mu nemi aure a wajen surukai nagari

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A duk lokacin da wani batu ya tashi kan matsalar auratayya, wani Hadisi ne yake yawan faɗo min a rai. Mattanin Hadisin na cewa, Ma’aikin Allah Mai Tsira da Aminci ya cewa sahabbansa, ‘Ku kiyayi ciyar da dabbobinku da ciyawar da ta fito a kan juji.’ Sai sahabbai suka tambaye shi abin da yake nufi da haka, sai Manzon Allah (SAWW) ya qara da cewa, ‘Ku guji aurar da ’ya’yanku ga dangin da basu da kyakkyawar shaida, masu munanan halaye.’

Saqon da za mu ɗauka daga wannan Hadisi shi ne cewa, idan za mu yi aure mu yi kyakkyawan bincike daga inda za mu aura ko mu aurar. Domin kaucewa ɗaukar kara da kiyashi. Wannan shi ne muhimmin saqon da darasin mu na wannan mako ya ƙunsa, muhimmancin bincike kafin aure, musamman game da halayen iyayen matar da za a aura, ko mijin da zai aura daga gare ku.

Masana ilimin halittar ɗan adam sun bayyana cewa, kowanne ɗa yana gadar wasu ƙwayoyin halitta da ake kira da chromosomes a turance, waɗanda su ne aka bai wa damar sarrafa halaye da ɗabi’u har ma da siffar yadda yaron da za a haifa zai kasance.

Waɗannan ƙwayoyin halitta su 46 ne, kuma kowanne jariri da za a haifa yana ɗauko 23 daga babansa, da wasu 23 daga babarsa. Kuma kowacce ƙwayar halitta da irin hali da ɗabi’ar da ta gado na kaka da kakanni, da ke nuna salsalar da iyayensa suka fito. Saboda haka ne addini ya wajabta mana muhimmancin yin bincike daga halaye da ɗabi’un iyalin da za mu auro mata ko miji daga cikinsu. Don a kaucewa gadarwa ’ya’yan da za a haifa munanan halaye ko wasu cututtuka da ake gadowa, daga ƙwayoyin halitta.

Zuzzurfan bincike kan wannan fanni na ilimi zai nuna maka yadda mutane ke gado wasu halaye daga iyaye da kakanni, wanda wani bai san da su a danginsu ko a jininsa ba, sai wani abu ya faru.

Fiye da rabin rayuwarmu na da nasaba da salsalar asalinmu. Kama daga halaye irin na kasuwanci, sarauta, ilimi, kyautatawa, sata, fashi, fasiƙanci, shaye-shaye, riqon aure, dabanci, da sauransu duk ana iya gadonsu.

A saboda haka, aure a gidan da babu kyakkyawar tarbiyya na iya shafar zuriyar da za a haifa, ba ma zaman auren kansa ba. Idan uwar mata ba tagari ba ce, ba mai kamun kai ba ce, ko ba mai biyayyar aure ba ce to, yana da haɗarin gaske aure daga ’ya’yanta, komai kyan surarsu ko iya soyayyarsu.

Haka idan uwa ƙazama ce, ko mai rashin kamun kai, marar riƙe sirri, akwai yiwuwar samun ’yar da za ka aura ta gado wasu daga cikin halayenta, komai wayewarta ko iliminta. Shi ya sa ma ka ke ji ana tsawatarwa kan auren ’yar mace, wacce ta girma ba tare da wani tsayayyen uba mai ƙarfin faɗa a ji ba, saboda fargabar da ake yi na ta girma cikin sangarta ko rashin ingantacciyar tarbiyya.

Wani rahoto da mujallar nazarin zamantakewa a Nijeriya ta fitar ya nuna cewa, duk da kasancewar babu ingantacciyar ƙididdiga game da adadin yawan saki ko rabuwar aure da ake samu a ƙasar nan, amma ƙiyasi ya nuna cewa, yawan rabuwar aure da ake samu a wasu jihohin Nijeriya ya zarce na wasu ƙasashen Turai.

Babu ma kamar jihohin da ke yankin arewacin qasar nan, inda Musulmi suka fi yawa, kuma babu tsauraran dokokin da ke hana saki cikin sauƙi.

A wani rahoto da tashar talabijin ta Aljazeera ta taɓa fitarwa an nuna sakamakon binciken da wakilinsu ya gudanar, inda ya bayyana cewa Jihar Kano ce kan gaba wajen yawan rabuwar aure.

Kaso mai tsoka daga wannan adadi na rabuwar aure da ake yawan samu na da nasaba da tsoma bakin surukai cikin zamantakewar auren ’ya’yansu.

Lokacin da auren Fatima Hassan (ba sunan asali ba ne) ya mutu bayan sun shafe shekaru biyar da mijinta Kamilu, jama’a da dama ba su yi mamaki ba, musamman waxanda suka san irin rashin jituwar da ke tsakaninta da babar mijinta, wacce tun farkon auren ba ta aminta da ita ba, saboda akwai yarinyar da ta so ɗan ya aura, wata ’yar ƙawarta, amma sam ya ƙi yarda ya dage sai Fatima.

Shi ma Ibrahim mai mata da yara biyar haka ya yi ta fuskantar irin wannan cin kashin da rashin zaman lafiya tsakaninsa da matarsa, saboda zugar da mahaifiyarta ke mata, kan ta ƙuntata masa ko ta hana masa kwanciyar hankali, matuƙar bai yi mata abin da take so ba, ko kuma ta kashe auren ta samu wani wanda ya fi shi wadata da abin hannu.

Duk da soyayyar da ke tsakaninsa da matar, Ibrahim ya sha tunanin rabuwa da ita don ya samu kwanciyar hankali, amma idan ya tuna da yaran da suka haifa da ita har biyar, sai ya ji ba zai iya ba, domin ba ya son yaransa su girma ba tare da ganin iyayensu na tare ba.

Bala, wani magidanci ne da yake fama da matsalar karayar arziki, da koma baya a harkokinsa na kasuwanci. Tun bayan da ya samu canjin rayuwa matarsa da ’yan uwanta suka shiga nuna masa wasu halaye na wulaƙanci da rashin mutunci, alhalin a baya sun fi kowa cin moriyar arzikinsa, fiye da ’yan uwansa na jini. Yanzu haka ba ya iya zuwa gidan surukansa ya gaishesu, ko kuma su idan sun zo gidansa ba ya jin daɗin haɗuwa da su, don irin yadda suke jefa masa maganganu na tozarci da gori kan haƙurin da suke cewa matarsa na yi na zama da shi cikin talauci.

Waɗannan misalai ne daga cikin matsalolin da ma’aurata da dama ke fuskanta, sakamakon rashin jituwa da surukansu mata, wanda a dalilin haka aure da yawa ya mutu, an haddasawa yara girma ba a gaban iyayensu ba.

Tsoma bakin iyaye cikin zamantakewar ’ya’yansu a gidan aure yana haifar da damuwa iri-iri a gidaje da dama. Abin takaici ne da ɓacin rai, ganin yadda wasu surukai ke shiga tsakanin ma’aurata, su yi ruwa da tsaki, a kan zamantakewar yaransu, har wata na yanke hukunci kan abin da za a yi a gidan ’yarta, ko irin abincin da take so a girka a gidan ’yarta a aika mata gida.

Wasu surukan su ne suke zavar makarantar da suke so a sa jikokinsu, wato ’ya’yan ‘yar su, ko kuma irin gidan da za su zauna a ciki, da ma wasu abubuwa da suka shafi sirrin zamansu na aure.

Ba abin mamaki ba ne, ka ga uwa ta sayi maganin mata ta aikawa ’yarta a gidan miji, ko ta je wajen wani malamin tsibbu ko boka, don ta karɓo wa ’yar asirin mallakar miji.

Wasu iyayen tun daga lokacin da ka ke neman ’yar su, za ka fahimci yadda suke katsalandan a soyayyarka da ita, tun ba ka fahimta ba har ka zo ka gane.

Wata uwar ce za ta riƙa zuga ’yar kan abin da za ta ce maka ko ta roƙa a hannunka, da ɗora maka wasu ɗawainiyoyi da ba su kamata ba, da suka shafi ’yan uwanta da ita uwar kanta.

Na ƙarfafa magana kan mahaifiyar mata ne, a maimakon uwar miji, saboda ƙorafe-ƙorafen da suke fitowa sun fi yawa daga ɓangaren mata, duk kuwa da kasancewar ’yan uwan miji ma dai ba baya ba.

Labarai game da muzgunawar uwar miji, sa’ido, zuga ɗanta ƙara aure, da uzzurawa matar ɗa a lokacin da aka samu jinkirin haihuwa suna da yawa. Mata da dama na rayuwa cikin ƙunci da rashin ’yanci, a gidajen mazajensu na aure, inda ba su dace da suruka tagari ba.

Akan ce idan kana neman aure in har uwar matar ba ta sonka to, ko da ita matar na sonka ba lallai ne ku samu zaman lafiya ba.

Haka kuma idan ’yar ce ba ta sonka, in har uwar na yin ka to, ka sha kuruminka kawai, abubuwa za su daidaita a hankali.

Amma kuma yaya abin yake a idan uwa da ‘ya suka haxe kai wajen ganin sun mallake mijin ko sun hana masa kwanciyar hankali, saboda wata buƙata tasu ko son zuciya da suke son cimma?

Hajiya Uwa Giɗaɗo Idris, wata marubuciya mai ba da shawarwari kan zamantakewar iyali ta shawarci iyaye mata su ji tsoron Allah, su daina zaluntar surukansu ko abokan zaman ’ya’yansu. Ta ce, ‘Kada mu bari duniyar mu ta yanzu ta hana mu lahiran mu ta gobe, a matsayin mu na mata.’

Fatan mu gabaɗaya shi ne a samu kyakkyawar fahimta a tsakanin ma’aurata da surukansu, don a gina al’umma mai cike da ɗa’a da biyayya, da girmama juna.

Surukai su daina zubar da girmansu a gaban ’ya’yan cikinsu, ko waɗanda suke auren ‘ya’yansu, su ma fa ‘ya’ya ne kamar kowa, kuma su ma nasu iyayen da ’yan uwan suna son su.

Mu taimaka wajen samun zaman lafiyar ’ya’yanmu a ɗakunan aurensu. Ta haka ne za su riƙa ganin mutuncinmu da girmamamu da ma neman shawararmu, a matsayin mu na iyayen matansu ko mazajensu.