Mun inganta tsarin shugabanci a Zamfara — Lawal

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa ta inganta tsarin shugabancin Jihar Zamfara da zummar bunƙasa jihar yadda ya kamata.

Lawal ya bayyana haka ne yayin taron majalisar zartarwar jihar wanda ya jagoranta ranar Litinin a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Gusau, babban birnin jihar.

Kakakin Gwmanan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar cewa, Gwamnan ya tunatar da mambobin majalisar ƙudurorin da gwamnatinsa ta sanya a gaba don cigaban jihar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, taron ya tattauna kan muhimman batutuwa bayan da Gwamnan ya gabatar jawabin maraba.

Sanarwar ta rawaito Dauna na cewa, “Yayin da ranar 28 Mayun 2024 ke ƙaratowa, ranar da za cika shekara guda a ofis, yana da kyau mu tattara bayanai kan ayyukan da muka yi al’ummarmu da kuma abubuwan da muke buƙata don ƙara himma a bakin aiki don shayar da mutanenmu romon dimokuraɗiyya kamar yadda muka yi musu alƙawari a lokacin neman zaɓe.

“Gwamnati za ta yi nasara ne kaɗai idan muka haɗa hannu muka yi aiki tare ba tare da mun farraƙa ba. Na sha faɗa cewa kamata ya yi mu dunƙule a yi aiki tare don cigaban jiharmu, kuma wanda duk ya ƙi ɗaukar kalamaina, ba ya tare da tawagarmu,” in ji Gwamna Lawal.