An gano gawar budurwar da aka sanar da ɓacewarta a Abuja

Daga BASHIR ISAH

An gano gawar Murjanatu Zubaiaru bayan da ‘yan uwanta suka ba da sanarwar ɓacewarta a Abuja.

Kafin mutuwarta, Murjanatu ɗaliba ce ‘yar aji huɗu a Jami’ar Abuja.

A cewar kawun marigayiyar, Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti kuma tsohon Mataimakin Shugaban Hukumar Kwali, a ranar Juma’ar da ta gabata Murjanatu ta bar gida zuwa makaranta amma ba a ga dawowarta ba, kuma wayarta ba ta shiga.

Ya ce, “Iyayenta sun tuntuɓe ni kan ko na ga Murjanatu alhali ba ta zo gidana ba kamar yadda aka yi zato. Duk ƙoƙarin da muka yi don ji daga gare ta waya, ya ci tura,’ in ji kawun nata.

Ana haka ne sai aka ga wani ɗan uwanta, Usman Garba Fodio, ya wallafa sanarwar rasuwar Murjanatu a shafin Facebook a ranar Litinin, inda ya ce an gano gawarta bayan da hatsarin mota ya rutsa da ita bayan ta tashi daga makaranta a ranar Juma’a.

Ya ce ana zurfafa bincike kan batun mutuwar marigayiyar.