
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun Sojojin Nijeriya na Birget ta 3, sun yi nasarar kama wanda ake zargi da ta’addanci da ƙwato makamai da wasu ababe a yayin wani samame a Ƙaramar Hukumar Ɗambatta da ke Jihar Kano.
Majiyoyin tsaro sun ce an gudanar da atisayen ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare a ranar 21 ga Yuni, 2026 bayan dakarun tsaron sun samu wani bayanin sirri akan wata maɓoyar ɓata-gari da ke ƙauyen Kwanan Dumawa.
A yayin atisayen ne aka yi nasarar kama mutum guda da kuma ƙwato ababe da dama daga wajen.
Cikin ababen akwai wata bindigar toka, ƙaramar bindigar gargajiya, bindiga ƙirar pistol, mazubin alburusai huɗu, wuƙaƙe uku, wayoyin hannu biyu, almakashi biyu, katin shaida, guru da kuma katin cirar kuɗi na ATM.
Majiyoyin sun ce a yanzu dai wanda ake zargin na hannun sojoji kuma ana cigaba da gudanar da bincike akansa.
Hukumomin soji sun ce, an ƙaddamar da samamen ne da nufin daƙile miyagun ayyuka da hana bazuwar ‘yan ta’adda a Jihar Kano da kewayenta.
Sun kuma jaddada ƙoƙarin sojoji na cigaba da ɗaukar matakan da suka dace wajen bunƙasa tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin da ma ƙasa baki ɗaya.
