
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya amince da samar da sabuwar gunduma da ta ƙunshi ƙauyuka guda takwas a Ƙaramar Hukumar Dandi da ke jihar.
Haka kuma, gwamnan ya amince da samar da sabon jagorancin ƙauye a Ƙaramar Hukumar Augie a matsayin wani ɓangare na ƙarfafa gwamnatin gargajiya da inganta shugabanci daga tushe a jihar.
Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomin da Sarauta, Alhaji Garba Umar Dutsinmari ne ya sanar da haka a wata takarda a Birnin Kebbi, ranar Alhamis.
A cewar kwamishinan, an kafa sabuwar Gundumar Buma ne daga Gundumar Dolekaina ta Ƙaramar Hukumar Dandi, inda aka naɗa Alhaji Salisu Hakimi a matsayin Hakiminta.
Ƙauyukan Buman sun haɗa da “Tunga Rafi, Gamana, Tudunsan, Gillare, Bump Town, Goraro, Bukki da kuma Alfarma Kwara,” inji Dutsinmari.
Ya ƙara da cewa, gwamnan ya kuma amince da naɗin Nasiru Umar Maizabo a matsayin Mai garin Marafan Garin Haruna a Gundumar Tiggi ta Ƙaramar Hukumar Augie Local.
Kazalika, Dutsinmari ya bayyana cewa, an gudanar da naɗe-naɗen ne bisa la’akari da hukuncin Sashe na 10 sakin layin A da B na kundin dokar Ƙananan Hukumomin Jihar Kebbi na 2008, wanda ya bayar da damar kafa gundumomi da naɗa hakimai.
A ƙarshe, kwamishinan ya yi kira ga sababbin jagororin gargajiyar da su kasance masu riƙo da gaskiya da adalci da nuna ƙwarewar yayin sauke nauye-nauyen da aka ɗora musu.
