Ranar matasa ta duniya: Mahdi ta yi kira da a ƙarfafa matasa domin gina ƙasa

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Wata mai fafutukar kare muradun matasa, Halima Ahmed Mahdi, ta yi kira ga gwamnatoci, iyaye, al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙarfafa matasa tare da samar musu da damammaki domin su taka rawar gani wajen ci gaban ƙasa.

Mahdi ta yi wannan kiran ne a cikin saƙonta na bikin Ranar Matasa ta Duniya ta 2026, inda ta bayyana matasa a matsayin wani muhimmin ɓangare na al’umma da ke da kuzari, buri da kuma damar jagorantar ci gaba.

Ta ce matasa da dama na neman ilimi da koyon sana’o’i, yayin da wasu ke da sha’awar shiga harkokin shugabanci, siyasa, kasuwanci da kuma ayyukan ci gaban al’umma.

Sai dai ta nuna damuwa kan yadda ake ware matasa da dama daga muhimman damammaki da hanyoyin yanke shawara, lamarin da ke sanya wasu daga cikinsu shiga hannun ’yan siyasa da wasu mutane masu amfani da su.

A cewarta, irin wannan amfani da matasa ba bisa ƙa’ida ba na iya jefa su cikin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, tashin hankali da sauran munanan ɗabi’u.

Ta buƙaci gwamnatoci da hukumomi da su samar da ingantaccen ilimi, horar da sana’o’i da kasuwanci, damammakin shugabanci da kuma hanyoyin da matasa za su shiga harkokin jama’a.

Haka kuma, Mahdi ta yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su samar wa matasa kyakkyawar tarbiyya, jagoranci da kulawa, yayin da ta buƙaci hukumomin tsaro da su riƙa hulɗa da matasa ta hanya mai kyau tare da ɗaukar su a matsayin abokan hulɗa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.

Ta shawarci matasa da su guji shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da tashin hankali, su mayar da hankali kan neman ilimi, koyon sana’o’i, kasuwanci da hidimar al’umma.

Ta ce, “Bai kamata a riƙa cewa matasa su ne shugabannin gobe kawai ba; ya kamata a ba su damar yin shugabanci, bayar da gudunmawa da kuma shiga yanke shawara a yau.”

Mahdi ta ƙara kira ga masu ruwa da tsaki da su “yi amfani da matasa cikin hikima da nagarta”, tare da ba su goyon baya da karramawar da suke buƙata domin su taka rawar gani wajen gina ƙasa.

Ta kuma yi kira ga matasa da su ɗauki alhakin makomarsu, su kasance masu kishin zaman lafiya tare da jajircewa wajen gina al’umma mai wadata da ci gaba.

By ukarofi

Leave a Reply