An buƙaci gwamnatin Gombe ta bai wa matasa masu sa-kai fifiko wajen ɗaukar ma’aikatan tsaro

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Ƙungiyar BREACH Initiative for Leadership Development ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Gombe da ta bai wa matasan da suka yi aiki a ƙungiyoyin sa-kai masu sanya kayan aiki na musamman fifiko a duk lokacin da za a ɗauki sabbin jami’an ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro.

Ƙungiyar ta yi wannan kiran ne a yayin gasar fareti da aka gudanar a Gombe domin bikin ranar matasa ta duniya ta shekarar 2026.

Da yake jawabi a wajen taron, tsohon daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA) a Jihar Gombe, Ado Solomon, ya ce mambobin ƙungiyoyin sa-kai masu sanya kayan aiki na musamman sun samu ƙwarewa mai muhimmanci a fannin ladabtarwa, aiki tare, hidimar al’umma da kuma wasu muhimman ayyukan tsaro.

Ya buƙaci gwamnati da ta yi amfani da wannan ƙwarewar matasan ta hanyar samar musu da damar shiga hukumomin tsaro na gwamnati.

Solomon ya kuma yi kira ga Sufeto-Janar na ’yan sanda, Rilwan Disu, ta hannun kwamishinan ’yan sandan Jihar Gombe, CP Ahmed Usman Chuso, da ya yi la’akari da ɗaukar ƙwararrun mambobin ƙungiyoyin sa-kai a lokacin ɗaukar ma’aikata domin rundunar ’yan sandan jihar da ake shirin kafawa.

Ya ce irin wannan mataki zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro a matakin ƙananan hukumomi da al’ummomi, tare da ƙarfafa gwiwar matasa su ƙara shiga ayyukan sa-kai da hidimar al’umma.

Da yake wakiltar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Abubakar Inuwa Kari, ya ce tsaro na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin jihar ta sanya a gaba.

Kari ya ce gwamnati tana goyon bayan kafa rundunar ’yan sandan jiha, yana mai cewa hukumomin tsaro da ake da su a yanzu sun yi wa nauyin da ke kansu yawa.

Ya tabbatar da cewa duk wani ɗaukar ma’aikata da jihar za ta taka rawa a cikinsa zai kasance cikin gaskiya da adalci, bisa cancanta, yana mai jaddada cewa ba za a mayar da harkokin tsaro abin siyasa ba.

Shugaban taron, Ibrahim Yusuf, ya yabawa BREACH Initiative da abokan hulɗar ta bisa shirya gasar, yana mai cewa taron ya samar da damar nuna ladabi, jajircewa da kuma hazaƙar matasa.

Yusuf ya kuma buƙaci gwamnati da ta yi la’akari da mambobin ƙungiyoyin sa-kai masu sanya kayan aiki na musamman wajen ɗaukar ma’aikatan tsaro a nan gaba, ganin irin ƙwarewar da suka samu a fannin ladabtarwa, aiki tare da hidimar al’umma.

A cikin sakon fatan alheri da ya gabatar, Capt. M.M. Nabinu ya ce ginshikin horon soja shi ne ladabtarwa, yana mai cewa fareti ba wai kawai nuna iya tafiyar da jiki cikin tsari ba ne.

Ya ce atisayen fareti yana koyar da aiki tare, kasancewa cikin shiri, juriya da kuma girmama umarnin da ya dace da doka, yana mai cewa gasar ta nuna irin nasarorin da za a iya samu idan aka horas da matasa yadda ya kamata kuma aka shirya su.

BREACH Initiative ce ta shirya taron tare da hadin gwiwar Youths O’Clock Gombe, Advocacy Centre for Development, da ma’aikatun tsaron cikin gida da harkokin cikin gida da kuma ma’aikatar kula da harkokin mata ta jihar.

Ƙungiyoyin sa-kai masu sanya kayan aiki na musamman guda 27 ne suka halarci gasar.

Boys Brigade ce ta lashe gasar da maki 87.67, yayin da Royal Ambassadors ta zo ta biyu da maki 87, sannan JIBWIS Jos ta zo ta uku da maki 85.33.

By ukarofi

Leave a Reply